Yawan amfani da wayar salula na sa karancin maniyyi a jikin Dan'adam - Binciken masana
Yawan amfani da wayar salula na taimakawa wajen kawo karancin ruwan maniyyi a jikin Dan'adam kamar yadda binciken masana a kasar Switzerland ya gano.
Binciken ya gano cewa matasa maza masu shekaru 18-22 da ke amfani da wayar salula sau 20 a rana, na a sahun gaba wajen haduwa da wannan hatsarin na karancin ruwan maniyyi.
Sau nawa kuke amfani da wayarku a rana?