Kumfar Fitsari
Me ke kawo Kumfar fitsari ?
Ganin kumfa a fitsari normal ne wani lokaci amman in ya zama kullun kullun mutum yana gani na lokaci me tsawo ya na nuni da alaman samuwar Protein a cikin firsari. Akan iya samun protein kadan a cikin fitsari wanda bai wuce 150mg ba a rana, hakan ba wata matsala bace.
š“ Fitan fitsari da karfi, in fitsarin mutum yana fita da sauri, zai iya forming din kumfa ko da babu protein sosai a cikin fitsarin.
š“ Matsalar Koda, In kodar mutum ta fara samun matsala sanadiyyan hawan jini ko qani rashin lafiya, hakan yakan sa ta kasa tace jini yanda ya kamata har protein ta wuce cikin fitsari.
š“ Urinary tract infection... infection a hanyar mafitsara, tun daga urethra, bladder, har zuwa koda..
š“ Dehydration... Rashin ruwa a jiki yakan sa fitsari ya zama concentrated saboda ruwan cikin fitsarin yayi kadan...
š“ Ma su yawan yawan motsa jiki
š“ Shan Maganin Zugi na Lokaci Mai tsawo. Irin su Diclofenac, ibuprofen, meloxicam Dssss
š“ dsss
In kana yawan ganin kumfa a fitsarin ka kuma ba wai yana fita da karfi sosai bane kuma kumfar bai warewa da wuri..... To ka fara da kara yawan ruwa da kake sha in bai bariba, kaje kaga likita don tabbatar da lafiyar ka musanman in akwai saura alamomin da suke nua cewa infection ne...
Allah ya kara mana Lafiya.. Amin.
Nr Imrana Shuaibu Adam
#Subyraan
#dehydration