Iyaye, Ga Matakan Tarbiyyar Yara:By Yusuf Shuaibu

Iyaye, Ga Matakan Tarbiyyar Yara:
By Yusuf Shuaibu 
 
 
Tarbiya wata kalma ce da ta samo asali daga Larabci, wacce ke nuni ga raino. Akasari ana amfani da kalmar ce don nuni da yadda muke kula da ‘ya’yanmu da kuma na kasa da mu a yayin da suke tasowa har su kai ga girmansu. Hakika, girma da muhimmancin kalmar tarbiyya sun wuce yadda muke amfani da ita a yau da kullun. Tarbiya ta banbanta daga al’umma zuwa al’umma, ma’ana, abin da ke da kyau ga wasu mutanen ba lalai ba ne ya zama yana da kyau ga wasu. Amma a gani na a kwai wasu abubuwa da za su dace da kowa, kuma su ne na kawo a nan zan yi dan sharhi a kansu, musamman hanyoyin da za a bi don inganta tarbiya yara.

Abu na farko shi ne, cusa wa yaro tsoron Allah. Hanyar cusa wa yaro tsoron Allah kuwa shi ne sanar da shi Allah da abin da ya yi umarni da abin da ya yi hani. A duk lokacin da yaro ya zama mai tsoron Allah da kokarin yin abin da Allah ya yi umurni da barin abin da ya yi hani, tarbiyarsa zai zamo mai sauki a wurin iyayensa, ko yaro na tare da su ko ba ya tare da su.

Cusawa yara son ilimi. Kasancewar ilimi shi ne ginshikin rayuwa, to hakkin iyaye ne su muhimmantar da ilimi wajen tarbiyar ‘ya’yansu. Su yi wannan ta hanyar maida hankali da ilmantar da ‘ya’yan nasu da kuma su kansu iyayen. Ya kamata su dauki ilimi a matsayin haske mai haskaka rayuwa ta ko wani fanni ba wai kawai don neman aikin abin duniya ba.
Dole iyaye su kasance abin koyi ga ‘ya’yansu. Ma’ana a nan duk wani abin da iyaye za su yi, ya kasan ce irin abin da suke son ‘ya’yansu su yi ne, domin shi yaro ya fi koyon abu a aikace fiye da abin da za a gaya masa. Misali in har uwa ba ta son yaranta su koyi zagi da tsinuwa to ta kiyaye zage-zage.

Iyaye su kasance masu girmama ‘ya’yansu. A al’adar malam Bahaushe, yara a na sa tsammani su kasance masu ji ne da biyayya amma ba su da ikon yin tambaya ko bada shawara. Wannan al’ada ba dai-dai ba ne. Ya dace yaro a karramashi kamar kowa ya zamanto yana da ta cewa a al’amura, sai dai manya su kasance masu kula da gargadi da dai-daita al’amura in za a kauce hanya. Yin haka na bai wa yara daman sanin darajar da suke da shi da kuma koyon yadda za a yi hulda da jama’a in an fita duniya . Girmama yaro yana daga cikin hanyoyin tarbiya sai mu kula.

Yawan kula da abin da yaro ke yi. A matsayinmu na masu kula da ‘ya’yanmu, ya zama lallai mu kula da duk wani abin da suke yi. Na san yana da wahala, amma wajibi ne in har ana son a yi tarbiya ta kwarai. Kula ba yana nufin hana su sakewa ba, sai dai yana nufin kasancewa kana/kina sane da inda suke ko abin da suke aikatawa dai-dai bakin gwargwadon iyawa a kowani lokaci. Wannan zai ba da ikon sanin halin da yaro ke ciki, sannan in ya yi ba dai-dai ba za a gyara masa.

 
Iyaye su guji yin munanan kalamai a kan yara. Kowa ya sani a addini mugun baki bai da kyau ga ‘ya’ya. Yaro idan ya sosa wa wasu iyayen rai, musamman iyaye mata, sai ka ji ana “Allah wadaran ka wane” ko “ la’ananne,” da dai sauran munanan kalamai wanda suna iya bin shi, sai ka ga yaro ya shiga yin taurin kai ba zai saurara wa kowa ba, ya zamanto bai da muntunci bai gani wani da mutunci, kuma daga karshe a rasa yadda za a yi da shi. Allah ya sauwake.

Koya wa yaro girmama na gaba da shi. In ka ga yaro na girmama na gaba da shi to ya gani a na yi ne. Iyaye dole su nuna wa ‘ya’yansu muhimmanci girmama babba ko daga ina mutumin nan yake, daga kauye ne ko daga birni, talaka ne shi ko mai dukiya ne, addinku daya ko ba addininku daya ba. Idan iyaye suka yi haka a aikace to yaro shi ma zai yi.

Koya wa yara kyauta ta hanyar aikatawa. Tarbiya ta kunshi rayuwa ce gaba dayanta, saboda haka komai ya kamata yana ciki. Kyauta aba ce mai kyau da yara ya kamata su fahimci cewar mutun ya zamanto mai yawan bayarwa ba wai mai yawan tsammani ba. Iyaye su kasance masu kyauta don nuna wa yara mahimmancin kyautar, misali ta hanyar aikensu su kai kyauta gidan dangi ko makwabta ko dai abokan arziki. Kuma kar a yarda a rika yin gori idan ambayar, saboda yara suna jin duk abin da iyaye suke fada kuma su ma in sun tashi haka za su yi.

 
Allah ya ba mu ikon tarbiyartar da ‘ya’yanmu ta hanya madai-daiciya.

Post a Comment

Previous Post Next Post