YANDA AKE AMFANI DA RUWAN SHINKAFA WAJEN GYARAN JIKIA yau ruwan shinkafa na ƙara samun karɓuwa a fannin

YANDA AKE AMFANI DA RUWAN SHINKAFA WAJEN GYARAN JIKI

A yau ruwan shinkafa na ƙara samun karɓuwa a fannin gyaran jiki, domin yana gyara fata da sanya fata sheƙi da santsi magance wasu matsolin fata.
Masu hada sabulai da mayuka na amfani da ita, abun burgewa shine zaki iya haɗa ruwan shinkafa a gida cikin sauki.
Ruwan shinkafa yana tattare da wasu sinadarai da suke gyara fata

👉 YANDA ZAKI 👇
1) TAFASAWA: Za’a samo shinkafa ko wace iri a wanketa (azubar da datti) sannan a zuba ruwa a tukunya sai a juye shinkafar a ciki a barta ta tafasa, sannan a sauke a tsiyaye ruwan a barshi yayi sanyi sai a zuba a mazubi.
Idan za’a yi amfani dashi sai a ɗiba a sirka da ruwa za’a iya matsa lemon tsami a ciki sai a rika wanke fuska da shi kamar sau hudu a sati.

2) JIƘAWA: Za’a samu shinkafa sai a zuba a roba a dauraye ta sai a nemi abu mai murfi a juye shinkafar a ciki sannan a zuba ruwa a rufe sai a barta na awanni idan ruwan ya yi fari sai a tsiyaye ruwan cikin gora a rufe.

@Domin Mata Dilka & Halwa

Post a Comment

Previous Post Next Post