AMFANIN GORUBA 10 ga lafiyar jikin dan Adam
Goruba wata bishiya ce da ta dade a duniya sannan an fi samun ta ne a kasashen Afrika. Bincike da aka gudanar akan goruba ya bayyana mamora da kuma alfanu da dama da take da shi, sakamakon sunadaran flavonoids, saponins da tananis, wanda wannan sunadaran ba sabon abu ne a wurin masana kiwon lafiya da likitoci.
Baya ga fa’idar ta wajen magance cututtuka ana amfani da ganyan ta wajen yin igiya, Kwando da tabarma.
Wannan ya sa muka binciko maku maganin cututtuka da Gorub ke yi a jikin dan adam.
Amfanin Goruba 10 ga lafiyar jikin dan Adam
1. Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.
2. Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.
3. Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a ji.
4. Goruba na maganin matsalar hawan jini.
5. Haka zalika goruba na magance cutar basir.
6. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
7. Cin goruba na kara karfin namiji.
8. Yana kuma rage kiba a jiki.
9. Cin goruba na kara karfin kashi da hakora.
10. Ruwan jikakkiyar goruba na tsiro da gashin mutum idan dai aka wanke kai da shi.