SHIN KO KUN SAN ?☆ Kodar mutum tana daya daga cikin muhimman sassan jikin dan adam.☆ Koda tana kama da siffar wake sannan kuma tana nan ne a bayan tunbi.

SHIN KO KUN SAN ?

☆ Kodar mutum tana daya daga cikin muhimman sassan jikin dan adam.

☆ Koda tana kama da siffar wake sannan kuma tana nan ne a bayan tunbi.

☆ Wadannan gabobin da ke da siffar wake suna da tsayin kusan inci 4 ko 5.

☆ Daga cikin ayyukan da koda keyi shine tana tsarkake jini da fitar da gurbataccen ruwa.

☆ Duka jinin da ke jikin mutum yana wucewa ta koda sau da dama a cikin yini.

☆ Wasu yaran ana haifar su da koda daya kacal. Yayin da yaron ya soma girma, wannan kodar guda ɗaya da sannu za ta kara nauyin da zai maye nauyin koda guda biyu.

☆ Koda tana tace galan 45 na jini a kowanne yini.

☆ Idan da za'a fitar da dukkanin nephrons da ke cikin koda a jera su, za su iya yin nisan kilomita 16.

☆ Kusan kashi 25% na jinin da zuciya ke fitarwa yana zuwa koda ne.

☆ Koda tana daukar kashi 0.5% na nauyin jiki duka ga matsakaicin ɗan adam.

☆ Koda guda daya mai aiki tana da tasiri wajen yin aiki kamar koda biyu ne a tare.

☆ A kowane minti 30, koda tana tace jini a cikin jiki sannan kuma ta fitar da ruwa mara amfani mai tarin yawa.

☆ Koda tana tacewa sannan kuma tana samar da fitsari kusan 1000ml zuwa 2000ml na fitsari.
Muna fitar da kusan 1.5 lita na fitsari a kowace rana.

☆ Kowace koda tana da nauyin kusan 4-6 ounces.

☆ Koda ta barin dama gabaɗayan tana da ƙanƙanta kadan idan aka kwatanta data barin hagu don samar da sarari ga bari mai fadi na hanta.

☆ lokacin da za'a yi maka dashen koda, ba'a cire tsohuwar koda, sai dai a kara da wata sabuwa akai. Don haka yawancin wadanda aka musu dashen koda suna ƙarewa ne da koda uku.

KADA KA KARANTA KA WUCE, KAYI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W).

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post