RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE, CUTA KO NI'IMA?AKWAI KARUWAR ZUBAR RUWA A GABAN MACE A LOKACIN SHA'AWA, MEKE SHIN MEKE KAWO WANNAN

RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE, CUTA KO NI'IMA?

AKWAI KARUWAR ZUBAR RUWA A GABAN MACE A LOKACIN SHA'AWA, MEKE SHIN MEKE KAWO WANNAN?
MAHAIFA DA BAKIN MAHAIFA SUNA ZUBAR DA RUWA GWARGWADON YADDA SINADARAI SUKE YAWO ACIKIN JINI.

TO AMMA LOKACIN DA MACE TAKE DA SHA'AWA, KUMA WANNAN SHA'AWAR BA DOLE BANE SAI LOKACIN JUMA'I BA.

KO WANI ABUNE KO WANI TUNANI DA ZATAYI DA ZAI SAKA MATA TA DAN JI WANI SHAUKI AJIKIN TA.

TO JIKINTA YANA DA SAURIN DAUKAR WANNAN ABUN, JIKI YA FARA SAKIN WASU NA'URORI ACIKIN JINI WADANDA ZASU SAKA GABAN MACE YA SAMU WANI CHANJI DAZAI SAKA ZUBAR RUWA YA KARU.

SHI KUMA WANNAN ZUBAR RUWAN KARUWA YAKE SABODA A LOKACIN DA TAJI WANNAN SHA'AWAR JINI GABAKI DAYA YA KARU ACIKIN JIKINTA, HAR ACIKIN KWAKWALWAR TA DA KUMA GABAN TA.

SHI WANNAN TARUWAN JININ SHI YAKAN SAKA SU WADANNAN KWAYOYIN DA SUKE DAIDAI BAKIN MAHAIFA DA WADANDA SUKE KUSA DA MAFITSARA SAI JINI YA KUME ACIKIN SU, SAI YA MATSE SU.

IDAN YA MATSE SU, SAI SU SAKI RUWAN DA YAKE TARE DASU, TO RUWAN NAN SHINE MACE ZATAJI TA JIKE A YAYIN DA TAKE JIN SHA'AWA.

KUMA SHINE MAFI YAWANCIN MUTANEN MU SUKAN CE MACE TANA DA NI'IMA.

TO ZAN BADA WANJ DAN MISALI.

A LOKACIN DA ZA'A CEMA MACE, IDAN KIN SHA KANKANA DA YAWA KO KUMA KIN SHA SAURAN KAYAN MATA SAI TACE TANA JIN KARIN NI'IMA, SAI TAJI DUK TA JIKE TA KASA.

BA WANI ABU BANE ILLA HANKALINTA DAYA KWANTA, TA SHIGA TANA IRIN TUNANIN DA ZAI SAKA TAJI WANNAN SHAUKIN AJIKIN TA.
TO A LOKACIN DA KUMA ZATAJI WANNAN SHAUKIN, WANNAN SAKON ZAI KAI GA KWAKWALWAR TA.

SAI KWAKWALWA TA SAKA SASSAN JIKI SU SAKI SINADARAI DA ZAI SAKA WADANNAN ABUBUWAN DA MUKAYI BAYANI DAKE GABANTA TA KUSA DA MAFITSARA SAI SU MATSE SABODA JINI YA TARU SAI SU SAKI WANNAN RUWAN, DAGA NAN SAI TAJITA TA JIKE.

WATA ZATA JIKE KADAN, WATA ZATA JIKE DA YAWA WATA MA BA LALLAI TA LURA DA JIKEWAR BAMA SABODA BATA SAKI JIKI BA SOSAI YAYI WANNAN TUNANIN.

WANNAN SHINE TAKAITACCEC BAYANI AKAN ABINDA MATAN MU SUKE KIRA NI'IMA, ACE MACE TANA DA NI'IMA.

KO TUNANI KO GANI KO SAURARO DUK SUNA IYA SAKA MACE TAJI WANNAN ABU DA AKE KIRA NI'IMA. 

DUK WADANNAN BAYANIN DA MUKAYI, NORMAL NE AJIKI IDAN KIKAJI WADANNAN ABUBUWAN. 

TO AMMA A INA NE ZAKI SAN CEWA WANNAN RUWAN DAKE ZUBA AKWAI MATSALA?

KAFIN MUYI BAYANIN WANDA YAKE ZUWA TARE DA MATSALA, BARI MU KARA YIN TSOKACI AKAN YANDA RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE BA TARE DA TAJI SHA'AWA BA DA YADDA YAKE CHANCHANZAWA DA BANBANCIN YANAYI DAGA FARKON WATA ZUWA KARSHEN WATA. 

TO ACE YAU KIN FARA AL'ADA (RANAR FARKO).
AL'ADAR KI YANA KWANA 5, KO 6, KO 7 JINI ZAI ZUBA.

BAYAN JINI YA ZUBA, ZAKI FARA GANIN CEWA KIN DAN BUSHE KADAN KWANA DAYA KWANA BIYU.

WANNAN HAKANE, HAKAN YA KAMATA.

SABODA GABAKIDAYA SINADARAN NAN DA MUKAYI MAGANA WATO OESTROGEN DA PROGESTERONE BABU SU AJIKIN KI.

DAGA LOKACIN DA AL'ADAR KI YA FARA, SAI JIKIN KI YA FARA SAKIN WADANNAN SINADARAN ACIKIN JINI SU KUMA SU FARA TASIRI A MAHAIFA DA BAKIN MAHAIFA. 
SAI KUMA WANNAN SINADARIN YAYI TA KARUWA ACIKIN JINI.

GWARGWADON YANDA YAKE KARUWAR GWARGWADON YADDA SHI RUWAN NAKI ZAI DINGA KARUWA YANA KARUWA.
SABODA HAKA BAYAN GAMA AL'ADA, RUWAN DA MACE ZATA DINGA GANI A GABAN TA YAKAN DAUKI KALAR KAMAR ACE KOKO KO MADARA.

HAKA ZAI CIGABA HAR YAYI KAMAR KWANA 5 DAGA NAN KAFIN TA KAI TSAKIYAR WATA LOKACIN DAYA KAMATA TA SAKI KWAI KENAN, TO SAI JIKINTA KUMA YA FARA SAKIN WANI SINADARI.

SHI KUMA WANNAN SINADARIN SHI YAKE SHIRYA GABAKI DAYA JIKIN MACE MAI YIWUWA SAMUN CIKI.

SABODA DUK LOKACIN DA MACE ZATA SAKI KWAI TO AKWAI YIWUWAR SAMUN CIKI, KUMA JIKI YANA SHIRYA MA WANNAN.

TO A LOKACIN DA MACE ZATA SAKI KWAI ZATAGA CEWA RUWAN DAKE ZUBA GABANTA YA KARA YAWA, SANNAN MAIMAKON YA FARA KALA KAMAR MADARA ZAI KOMA KAMAR RUWAN KWAI, KAR KAMAR RUWA AMMA KUMA YANA DA YAUKI KO ACE KAMAR RUWAN KUBEWA AMMA WANDA YA DAN FISHI KAURI.

TO WANNAN CHANJIN YANA FARUWA A LOKACIN DA MACE ZATA SAKI KWAI KUMA DUK YANA KOKARIN YA TAIMAKA NE TA YADDA IDAN TA SADU DA NAMIJI SHI KWAYAR HAIHUWAR NAMIJI ZAIYI SAURIN HADUWA DA NATA KWAYOYIN HAIHUWAR SABODA A SAMU JUNA BIYU.

IDAN MACE KUMA BATA SADU DA NAMIJI BA KO KUMA BA'A SAMU JUNA BIYU BA AMMA TA SAKI KWAN, SHI KUMA SATI BIYUN KARSHE ZA'A SAMU CHANJI NA RUWAN DAKE ZUBA A GABANTA. 

SAI YA FARA RAGE YAWA, YANA RAGE YAWA.
HAR SAI YAZO YANA KOMAWA WANNAN KALAR MADARAR NAN KO KALAR KOKO DA MUKAYI BAYANI. 
ZUWA KWANA 3 ZUWA 5 KAFIN AL'ADAR TA YAZO SAI TAJITA KUMA TA KARA BUSHEWA, DAGA NAN KUMA SAI AL'ADA TAZO. 

TO YANZU JINI YAZO MATA, SHIKENAN AN GAMA WATAN.

ASHE MACE TACE KO YAUSHE KO TAJITA KWATAKWATA BATA ZUBAR RUWA KO KUMA TACE RUWAN YA CHANZA KALA DA YANA ZUWA KAR KAMAR RUWA YANZU KUMA YA DAWO KAMAR KOKO.

ASHE DUK BA WANI MATSALA BACE BA.

A LOKACIN DA MACE ZATA FARA TSAMMANIN RUWAN DAKE ZUBA A GABANTA MATSALA NE SHINE IDAN:

NA DAYA TAGA YA KARU DA YAWA AKAN YADDA TA SABA.

AI AKWAI MACE SABBABIYA, ABINDA ZAKI GANI YAU WANNAN WATAN YAZO, WANI WATAN YAZO WATA MAI KAMAWA MA YAZO, KO YAUSHE KINA CIKIN SHI WATO YA ZAMO KIN SABA DASHI BA MATSALA BACE.

AMMA IDAN KIKA GA YA KARU FIYE DA YADDA KIKA SAN SHI, TO AKWAI MATSALA. 
KUMA KAMAR YADDA MUKA FADA CEWA AKWAI MACEN DA ITA RUWAN DA TAKE ZUBARWA KADAN NE BADA YAWA BANE.

AKWAI KUMA WACCE HAKA NAN BA TARE DA WATA MATSALA BA RUWAN DA TAKE ZUBARWA ZAI IYA YAWAN DA HAR SAI TA SAKA WANI ABU TA TARE SHI.

AMMA IDAN KIKA GA YA WUCE HANKALI YADDA KIKA SABA DASHI, TO KI TUNTUƁI LIKITA SABODA ZAI IYA YIWUWA AKWAI WATA MATSALA.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

DUK WANDA YA FA'IDANTU DA WANNAN RUBUTU YAYI MINI ADDU'A. 
SAI MUN HADU A RUBUTU NA GABA.

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post