Wasu matan idan sun haihu bayan sun samu ƙaruwa basa yarda a musu ɗinki a asibiti. Shawara ko a gida kika haihu to ki ziyarci LIKITAR MATA a asibiti domin a duba ki da kyau

Wasu matan idan sun haihu bayan sun samu ƙaruwa basa yarda a musu ɗinki a asibiti. Shawara ko a gida kika haihu to ki ziyarci LIKITAR MATA  a asibiti domin a duba ki da kyau... Sannan halittar mata ba ɗaya ba kowace mace da yadda Allah ya halicceta.
DAGA WSIƘUNKU!!!

Assalamualaikum

Mama tambaya nazo da ita don Allah ki yimin posting

Bazawara ce tayi aure kwata kwata haihuwarta biyu ta fito sai ta Kara sabon aure yanzu mijin yace gabanta kamar kofar gari yake bazai iya zama da ita ba Yana ta mata walakanci yace baya samun gamsuwa da ita Yana da wata matar da yaya sun Kai biyar Amma yafi samun nutsuwa da Mai yaya biyar dinnan don Allah a tambaya mana Maza mussam masu mata fiye da guda daya Hakan zai iya faruwa ko Kuma kawai walakancin mijinne sannan idan ya rabu da ita yarinyar me haihuwa biyu akan wannan dalilin yayi laifi ko baiyi ba

Dan uwana ne na masa fada akan Yana walakanta Amaryar shine yamin message ya fada min kaina ya kulle kwata kwata auren baiyi wata biyar ba Amarya tana kokarin zama bora akan Mai haihuwa biyar. (Sannan akwai halitta) maza kuji tsoron Allah.

Don Allah Maza masu mata fiye da guda daya su bamu cikekken bayani da Kuma mata masu ilimin Hakan musamman ku marubuta nasan Kuna samun kes Mai kama da haka.

LIKITAR MA'AURATA...✍️✍️✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post