SHAWARA GA MA'AURATA DA WADANDA ZASUYI AURE ANAN GABA

SHAWARA GA MA'AURATA DA WADANDA ZASUYI AURE ANAN GABA

Magidanta da yawa sune dena ganin kyan matansu na aure, suna dena jin tausayi, jin kai da dena kyautata wa matansu saboda wasu dalilai, manyan dalilai daga cikinsu shine auren sha'awa da auren kyawun fuska ko dirin jiki, ita kuwa sha'awa dama ana kasheta ne a watanni uku da yin aure

Duk wanda zai auri mace saboda haka to tsanani ka shekara guda da ita a samu ciki ta haihu ta fara shayarwa, daga nan tsana ne da wulakanci zai biyo baya har illa Masha Allahu

Dan uwa, ka tabbata ka auri mace don kana kaunarta, kauna na gaskiya wanda duk abinda zai faru na tawayar halittar jiki ba zaka iya jin sonta ya ragu a cikin zuciyarka ba

A lokacin da Magidanci ya ji ya dena son matarsa, zai fara wulakantata,  daga nan hankalinsa zai koma ga matan banza  a waje, to kofar barna da halaka da tabarbarewan rayuwa ta budu a gareshi

Babu abinda yake saurin susuta rayuwar Magidanci sama da neman matan banza a waje, ko da wasa kar ka yadda bayan kayi auri a wayi gari ka fara sha'awar matan banza a waje

Ka sani, su matan banza; karuwa mai zaman kanta, ko karuwa da take karuwanci a gaban iyayenta, kudi take kashewa ta gyara jikinta don tayi dadi ko ta burge 'yan iska da fasikai

Kuma a gurin mazan banza karuwa take samun kudin gyaran jiki, me zai hana kudin da zaka bawa matar banza ka koma gida ka kashe kudin wa matarka na Sunnah don ka samu abinda kake so a jikin mace?

Ka sani, duk abinda matar banza a waje take da shi a halittar jikinta da yake rikita maza matarka ma tana da shi a gida, me zai hana ba zaka kashe mata kudin gyaran jiki ka samu abinda kake so ba?, uwa uba ga lada

Akwai wata khudubar banza da fasikai sukeyi, suna cewa wai "gyadan kale yafi dadi" ma'ana matar banza a waje tafi matar cikin gida dadi, wannan khudubar shaidan ne da kuma yaudara, saurari bayanin da nayi cewa kudin da zaka kashe wa matar banza ka koma gida ka kashe wa matarka, sai kaji tafi matar banza dadi

Samari da baku taba aure ba, ku rike wannan jawabin da kyau, zai amfaneku matuka

Muna rokon Allah Ya kare mu daga fadawa tafarkin halaka 🙏

Post a Comment

Previous Post Next Post