AUREN KISAN WUTA HARAMUN NE :Auren kisan wuta wani irin aure ne da akan yi ba da niyyar zama ba ,sai don kawai a halattawa mijin da ya saki matar ta koma gurinsa tunda a ka'aida idan ya saki matarsa sakin da babu kome to dole sai wannan matar ta yi wani

AUREN KISAN WUTA HARAMUN NE :

Auren kisan wuta wani irin aure ne da akan yi ba da niyyar zama ba ,sai don kawai a halattawa mijin da ya saki matar ta koma gurinsa tunda a ka'aida idan ya saki matarsa sakin da babu kome to dole sai wannan matar ta yi wani auren kafin ta dawo gurinsa.
Akan yi irin wannan auren da sharadi. Ma'ana ma'auratan sun yi sharadin rabuwa. Ko a yi sharadi da mai auren cewa zai aure ta amma zai sake ta. Wani lokacin kuwa ita matar ita take lallaba wani ya aure ta amma ita niyyarta bq zama tare da shi ba. A'a so kawai take idan ya sadu da ita ta kunna masa tilas dole ya sake ta.

Ko ma dai yaya abin yake irin wannan aure haramun ne kuma batacce ne a gurin malamai masu yawa  , yaudara ne kuma cin amana ne. Sawaun an yi shi da sharadi ko a'a. Ta bangaren mijin shi kadai ko ta bangaren matar. Hatta malaman da suke ganin idan mace ta yi ba da niyyar zama ba aureen ya yi sun yadda cewa ta wani bangaren ta aikata haramci kuma ta yi yasudara ta ci amana. Sannan zai wahala auren ya yi albarka kuma babu jimawa za'a iya komawa gidan jiya. Mw'ana ko ta koma gidan mijin na ta ba zata canja zani ba.

A takaice dai dukkan malamai sun yarda cewa auren kisan wuta haramun ne domin yq saba dq dukkan wata aya ko Hadisi da suke magana akan aure.
Duk inda Allah da Manzonsa suka yi magana akan aure ko saki to suna magana ne akan da aka yi shi da niyyar zamq mutu  ka raba.
Duk wani aure da aka yi da yaudara ko karya da wahala ya yi albarka. Idan ma an yaudari mutum to ai ba za'a yaudari Allah ba
Malamai dake bayar da fatawar mace zata iya yi idan ba sharadi su ji tsoron Allah domin ko ba komai duk cikinsu babu wanda zai so a yaudare shi. A aure ba don ana sonsa ba.
Waliyyan ma'aurata su ji tsoron Allah su daina goyawa yayansu baya akan lamarin kisan wuta.

Mata kuma su sani idan mijinsu na farko ya sake su ba da hakki ba Allah zai saka musu kuma zai canja musu da mafi alheri daga shi.
Dabara , wayo da yaudara ko cin amana basa warware matsala sai dai su karata.
Tsoron Allah da dogara gare shi , gaskiya da rikon amana su ke warware matsaloli.
Allah ka azurta mu da su.

Abu Abdullah
Hamza Uba Kabawa.
27/ Zul Hijja/1445
4/July/2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post