hanyoyin sarrafa filawa

Zamu fara girke-girken mu akan abincin da ake da filawa. kowa yasan filawa wacce a keyin fanke, cincin, ko kek da ita.

Akasarin girke-girken filawa yana zama ko a gasa a cikin oven ko a soya acikin mai.
Sirrin kwava filawa

Duk kayan da zakiyi amfani dasu suzama masu sanyi, Abin nufi a nan kada abar filawa ko butter ko yeast ko baking powder a wuri mai zafi ko rana. Kafin yin ko wane irin abinci na filawa.
Kada a saka baking powder ko kuma yeast ya yi yawa ko kadan.
A tankande filawa kafin kowane girki.
Wajibi ne abar kwavi ya huta har zuwa minti 20-30, kafin afara aiki dashi.
Kada a saka butter ko sugar yayi yawa yana hana kwavi tashi.
PUFF-PUFF
Kayan hadi:-
•Filawa
•Suger
•B/powder ko yeast
•Kwai
•Ruwan zafi
•Man gyada
•Maggi/Gishiri
•Madarar gari.

YADDA AKE HADAWA
Kwaba filawa da yeast, kwai, madara amma kada yayi ruwa ko tauri.
A yi rolling dinshi (kamar ball), a soya a mai mai zafi.
Idan ya soyu a barbada masa sukari.
PAN CAKES WITH HONEY
Kayan hadi:-
•Filawa
•Baking powder
•Gishiri
•Kwai
•Butter ko Mai
•Madarar ruwa.

YADDA AKE HADAWA
Kwaba filawa da kwai, Gishiri da madara har sai kwavin yayi ruwa-ruwa (Ana amfani da madara a matsayin ruwa) .
Zuba mai ko butter acikin kasko idan yayi zafi sai kidinga zuba kwavavviyar filawa ana soyawa, amma banda juyawa kamar dai yadda ake sinasir.

SHORT BREAD BISCUITS
Kayan hadi:-
•Filawa
•Suger
•Butter
•Gishiri
•Kwai.
YADDA AKE HADAWA
Kwava filawa da kwai, butter da kuma sugar amma kadan sabida za’a saka a wurin murji, kwava kamar yadda ake kwavin cin-cin. Goge katakwan murza meat pie barbada sugar akai sai a rinqa murza kwavin akan sugar din, idan yamurzu sai a samo gwan-gwanin cake amma qanana sai a rinqa sawa ana fidda (shape) dashi. Idan angama sai a shafa kwai akai, a gasa a cikin oven.
FLOUR BALLS IN STEW
Kayan hadi:-
•Filawa
•Ruwa
•Kaza ko Nama
•Maggi ko [spices]
•Tafarnuwa [mint]
•Albasa mai lawashi
•Mai
•Tumatir (Tomtos)
•Tattasai ko Attaruhu
.
YADDA AKE HADAWA
Kwava filawa da gishiri da mai acikin kwano ayi kwavin ruwa-ruwa, ajiye gefe daya. Zuba kaza ko nama acikin tukunya, ruwa, Gishiri, albasa da citta har sai sun dahu. Idan ruwan yadan tsotse, zuba timatir da attaruhu yayi dan romo romo. Sai a rinqa zuba wannan kwavin acikin miyar da kadan da kadan (kamar sakin dan wake) har sai angama zubawa, rufe tukunya har zuwa dan mintina idan ya dahu a sauke. Amma za’a ci da zafinsa kafin yahuce.

SAMOSA
Kayan hadi:-

•Filawa
•Butter
•Gishiri
•Mai
•Nikakken nama
•Albasa
•Koran tattasai
•White pepper
•Thyme
•Curry

YADDA AKE HADAWA
kwaba filawa da mai ko butter,gishiri da ruwa kamar na meat pie.
rufe ajiye har zuwa minti 20.
raba filawa gida 4.
murza vari daya kan katakwan yanke yanke (Chopping board) har sai tayi lafai-lafai. kada yayi kauri sai a shafa man gyada akai da burushi irin na masu fenti dan karami (Pastry brush).
sake dauko wani varin na filawa murza shi kamar yadda aka yiwa na farko.dura shi saman wancan da kika shafawa mai kuma murzawa.itama shafa mata mai.haka za ki tayi har agama gaba daya (ana shafa mai dan kada su manne da jikin su). idan anzo na karshe sai asa filawa.
shafa mai a cikin tire irin wanda ake dora cake aciki. dauki kwabin a hankali daura kan tiren. kunna oven ki matsa kaicin zafi (moderate) har zuwa minti 20. Ko kuma idan anga ya fara dagowa yana rabuwa da junansa. fito dashi sai a yanka gida biyu dai dai. sai a nadeshi kamar kwakkwaro zuba nama aciki rufe bakin da filawa da’aka kwaba da ruwa. soya cikin mai mai zafi.
yadda ake soya naman cikin samosa. zuba niqaqqen naman a kasko da Maggi/Gishiri, tafarnuwa, w/pepper da mai kadan idan naman ya soyu zuba albasa da koran tattasai sauke.
CAKE
Kayan hadi:-

•Filawa
•Madara
•Kwai
•Flavor
•Baking powder
•Butter
•Suger

YADDA AKE HADAWA
zuba kwai da suger a cikin (whisker) har sai yayi ruwa-ruwa yazama fari,ya hadu sosai.
zuba kadaddan kwai a ciki cigaba da juyawa,har su hadu sosai.sai ki zuba filawa da aka tankade ta da baking powder kina juyawa a hankali,zuba madara da flavour juya sosai.

Post a Comment

Previous Post Next Post