kotun koli ta yanke hukuncin ci GABA d'a amfani da tsofaffin kudi

Kotun ƙoli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗi
03/03/2023 Muhsin Gambo Dauda
Kotun ƙolin Nijeriya, ta yanke hukunci ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin har zuwa 31 ga watan Disamba bana.

Yayin yanke hukuncin a yau, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar babban bankin kasa CBN ta tanada, wadda ta ce, kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin halastaccen kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.

Kotun ta kuma soke matakin gwamnatin tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.

Freedom Radio ta ruwaito cewa, Wasu gwamnonin ƙasar nan ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar tsarin sanya wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗin.

Post a Comment

Previous Post Next Post