Kotun Shari’ar Musulunci dake zaman ta a filin Hokey, ta yankewa Murja Ibrahim Kunya hukuncin sharar Asibitin Murtala na tsahon sati uku, tare da yin bidiyo na neman afuwar Al’umma cikin kwanaki biyu kan abinda ta aikata
Kazalika kotun ta yankewa Idris Ashiru mai wushirya da Aminu Ibrahim BBC da Sadik Sharif Umar hukunci share Masallacin Murtala na tsahon makonni uku.Jami’an ƴan sanda a jihar Kano, sun cafke fitacciyar ƴar TikTok ɗin nan Murja Kunya.
Rahotonni sun bayyana cewa, jami’an sun kama ta ne a otal din Tahir lokacin da ta je domin kama wa baƙin da za su ziyarci Kano domin taya ta shagalin zagayowar ranar haihuwartaJaridar Solacebase ta ruwaito cewa, a watan Satumban bara ne wata kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano wasika da ya kama da bincikar Murja Kunya tare da wasu ƴan TikTok bisa zargin lalata tarbiyyar matasa.
Sauran sun haɗa da Mr 442 da Safara’u da Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Sarki da Ado Gwanja sai Ummi Shakira da Samha Inuwa da kuma Babiana.Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, a watan Satumban bara ne wata kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano wasika da ya kama da bincikar Murja Kunya tare da wasu ƴan TikTok bisa zargin lalata tarbiyyar matasa.
Tags:
New