Assalamu alaikum jama’a, a yau na zo muku da yadda ake hada jus din kankana.
Za a iya yin shi domin sayarwa ko kuma domin sha a gida ko biki.
KAYAN HADI
Kankana
Sukari
Madara
Flavor
Yadda Ake Hadawa
A yanka kankanar a zuba ta a blender a markada ta sosai ta yi sumul babu sauran gudajin kankana.
A tace markadaddiyar kanakar sosai sannan a zuba sukari daidai bukata a ciki.
Daga nan sai a zuba madarar ruwa da flavor cikin chokali a cikin kankanar da aka tace sannan a jujjuya.
Idan an gama sai a sa a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a sa kankara a ciki gwargwadon yadda ake so a sha.
Tags:
food