Abubuwan da zakiyi domin samun dawwamammiyar niima

Abubuwan da zakiyi domin Samun dawwamammiyar Ni'ima.


Shan ko wane ruwa daga cikin wadannan ya na saukarwa da mace ni’ima mai kyau, kuma ko wanne ruwa akwai yadda a ke sarrafa shi da mahadan da za su sa kiji dadi.







Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga ciki:
1) Ruwan Kankana, Ayaba Manya Uku, Kankana Kwata da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya yi sanyi, ku sha kamar juice ke da maigida. Ya na karin ni’ima.





2) Ruwan Tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa ki ci. Shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da saka jin dadin auratayya, sannan hakan ya na saka gogewar fata.





3) Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fidda dusar. 





Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya. Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki. 





Ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki barshi ya kwana. Hmmm zumdum! Ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, uwargida za ki ban labari.
4) Ruwan Zogale: Amfanin ruwan Zogale ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikkunanmu ne kawai.





A- ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan zogalen ki zuba kaninfari da citta ki tafasa. Sai ki sauke ki dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya saukar da ni’ima sosai. Ya na karawa mace kuzari a jikinta sosai, sannan ya na karawa mace juriya wajen saduwa.





B- Ki tsinke zogale ki wanke ki markada ganyen a ‘blander’ ko ki mutstsika da hannunki ki kara ruwa a kai ki tace ki matse dusar. Ki zuba madarar ruwa gwangwani daya a cikin ruwan zogale cikin jug daya. Ki sa zuma ta ji sosai. Ki juya ya hadu ki dinga sha. Gaskiya ba shi da dadin sha, sai dai akwai shi da aiki; ni’ima lutsutsu! Domin duk bushewar gabanki da rashin ni’imarki sai ni’ima ta zo, kuma ya na sa jin dadi sosai.







C- A nan ganyen zogalen da ki ka tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku ,ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa kulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano gurin maigida.





5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa. Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai.





 Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da shan ki za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu da son kasancewa da maigidanki. Za ki ji dadin da ki ka dade ba ki ji ba. Maigida kuwa zai gamsu da ke sosai.







6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog daya. 







Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Maigida zai dinga jin dadinki ya na gamsuwa da ke sosai. Tsimin rake kenan.

Post a Comment

Previous Post Next Post