*TUWON SHINKAFA DA MIYAR DANYEN ZOGALE*
Abubuwan buqata👇🏾
Shinkafa
Ruwa
Da farko zaki wanke shinkafarki ta ki jiqa ta ta dauki kaman minti 30 a ruwa.
Sai ki dora tukunya a kan wuta ki zuba ruwa dai dai Wanda zai dafa miki shinkafar ki, in ya tafasa saiki dauko wannan shinkafar taki da kika jiqa ki Zuba a cikin ruwa ki barshi yai ta dahuwa har sai yayi laushi sosai sai ki dauko muciya ki tuqa sosai yayi kyau.
Sai ki barsa ya turara Bayan nan sai ki bude leda ki kwashe tuwon ki zuba a food flask.
✍🏾 Gloden kitchen👨🏾🍳👩🏾🍳
*MIYAR DANYEN ZOGALE*
Abubuwan buqata👇🏾
Nikakken kayan Miya
Ganyen Danyen zogale
Gyada
Citta
Tafarnuwa
Maggi
Curry
Kayan kamshi
Gishiri
Nama/kifi/ganda (optionals)
Manja
Da farko zaki wanke naman ki tafasa shi da kayan kamshi da gishiri,bayan kin tafasa ki soya ki ajiye a gefe,sai zaki zuba manja,albasa da nikakkiyar danyen citta a tukunya ki soya da ya fara qamshi sai ki dauko markaden Kayan miya ki zuba ki Dan saka baking powder saboda kar yayi tsami bayan nan sai ki dauko kalan maggi da kike buqatan,curry,thyme,da gishiri dinki ki soya miyar ki dashi dama kin soya gyadar ki sama-sama kin nikata ta zama gari sai kidan kwa6ata da ruwa ki ajiye,sai wanke ganyen zogalenki wanda kika gyara ki zuba ki karasa soyasu a tare da kayan miyan su dahu in miyar ya soyu sai tsayarda ruwan sanwarki daidai yanda miyan ba zaiyi ruwa ba,bayan miyan ya tafasa ruwan ya rage Sai ki zuba kwa6a66iyar gyadarki ki juya su hade jikinsu,Sai ki rife ta karasa dahuwa ki sauke... Shikenan an kammala.Sai dai kowa da yanayin YANDA yake yin nashi. Kunsan ilimi kogi ne.
Tags:
food