Yawan Aikata wadannan abubuwan guda Bakwai (7) na sanya Fata saurin tsufa da yamushewa.
Kowane mai rai dole ne wata rana ya tsufa. Amma akwai abin da in aka yi wa fata zai sanya ta tsufa da wuri. Kuma dole ne mu yi iya kokarin barinsu. Abubuwa da suka hada da rashin bacci da yawan gajiya da amfani da kayan kwalliyar da ba ta dace da fata ba. Yawan shan taba da kuma yawan cin naman shanu bayan an bai wa shekara arba’in baya.
1)- Gajiya: Yawan gajiya da shiga damuwa na matukar sanya fatar jiki tsufa. Idan mutum ya shiga damuwa, fatar na fitar da wani abu ‘cortisol’. Wannan ‘cortis’ din yana yi wa fata dameji. Sai a ga mutum ya tsufa da wuri. Shi ya sa sai a ga wanda yake cikin damuwa da talauci yana riga sa’anninsa tsufa da ke birni, kuma cikin jin dadi. Don haka sai a yi iya kokarin rage sanya kai tunani da damuwa.
2)- Kayan kwalliya: Akwai wasu kayan kwalliya da ke dauke da sinadarai kamar su; zinc odide da dimethicone da propylene suna iya sanya fata tsufa, musamman idan an yawaita amfani da su. Wasu sinadaren suna bata fuska kaikayi daga nan sai fesowar kuraje har fuska.3)-Taba: Yawan shan taba na sanya tsufar fata da wuri domin wannan sinadarin da ke cikin sigari nicotine, wanda ke toshe magudanar jini. Shan tabar na sanya fata ta sake karfinta. A rage shan taba saboda tana janyo tsufar fata.
4)- Yawan cin soyayyen abinci da cin abinci a kan kari ba don yunwa ba na sanya fatar jiki kiba, kuma hakan zai janyo fatar fuska cika, sai a ga mutum tsabagen kiba ya fi shekarunsa.
5)- Yana da kyau mutum ya san irin nau’in fatarsa kafin ya yi amfani da kowane irin sabulu. Idan sabulu bai dace da fatar mutum ba, zai iya sanya tsufan fata.
6)- A rage cin abinci mai dauke da mai, musamman idan shekaru sun ja. Bai kamata idan an kai shekaru arba’in a rika cin naman shanu ba. Yawan cin irin wadannan abubuwa yana janyo ciwon kafa da sanya mutum tsufa.