AMFANIN SAIWAR ZOGALA
Saiwar zogala nada matukar amfani ga lafiyar dan adam domin masana sirrin magunguna sukanyi amfani daita sosae wajen sarrafa magunguna dadama domin riga kafi ko warkar da wasu cuttukan dake addaba alumma amma yanzu zamu kawo maku wasu magunguna da saiwar zogala keyi wanda suka hada da.
(1) SANYIN JIKI
A tauna saiwar zogale tare da citta kwara daya.
(2) TSUTSAR CIKI
A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.
(3) CIWON SANYI
A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.
(4) YAWAN MANIYYI
A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.
(5) TARI KO MURA
A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.
(6) RAGE NAUYI KO IBA
A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum
(7)ZAFIN FISTARI
A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.
(8 ) CIWON SUGAR
A rinka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.
(9) QAZUWA
A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha
(10) CIWON DAJI CIKIN BAKI
A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dashi a kullum sau uku, safe da rana da yamma
(11) CIWON YASTA DAN KARKARE
A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.
(12) CIWON KAI MAI ZAFI
A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.
(13) KARIN NIIMA GA MATA
A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara a sha.
Yanuwa muna rokon duk wanda ya karanta wannan sako da yayi kokarin watsama duniya domin amfanuwar yanuwa musulmi.