GUDUMUWAR AMARYA GOBE KI GYARA*
*DOMIN MASU SHIRIN AURE GOBE*
*_▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒_*
*_❀ HADIN NI'IMA ❀_*
_aya_
_dabino_
_mazarkwaila_
_hakin daka_
_madara ko nono mai kyau_
*YANDA AKE YI ZAKI*
sami ayarki ki tsinceta tas sannan ki wanke ki shanya, idan
ta bushe sai
ki zuba a turmi ki dakata lukwi, ki na dakawa kina
tankadewa da rariya mai
laushi, sanya amarya kuka sai ki daka dabinonki da cukwi
da mazar kwaila da
hakin daka lukwi ki hada da dakakkiyar ayarki guri guda, ki
sami mazubi na
roba mai kyau mai murfi ki zuba, duk sanda zaki dinga sha
sai kisa madara
peak ko kuma fresh milk danyen nono ko yoghurt me kyau,
ba a bawa yaro
mai kiwa.
*▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒*
*_■ HADIN NI'IMA 2 ■_*
❍ aya
❍ dabino
❍ tafarnuwa
❍ sugar da madara
YADDA AKEYI
zaki sami ayarki ki jika ta ta jiku sannan ki surfata, ki jika
dabinon ki shi ma
ya jiku sosai sai a markada da dan blander ko kuma a
markado a inji amman kice sai an gama nikan gero sannan
za'a nika miki don kada a nika a kan kayan miya don kada
yayi yaji, sai ki zuba garin tafarnuwa a kai sai ki hada
da madara ko nono idan da hali a saka a firji yayi sanyi ko
kuma a sanya kankara a kai a sha ba a bawa yaro.
_▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒_
*_✰ HADIN NI'IMA 3 ✰_*
_gwanda_
_kankana_
_abarba_
_lemon zaki_
_kankara_
_sugar_
YANDA AKEYI
zaki sami gwandarki da kankanarki da abarba da ayaba ki
yayyanka gwitsi
-gwitsi kamar kan kuda ' inji yara- sai ki bare bayan lemon
zaki ki shima har
da wannan farar fatar ki cire kwallayen suma sauran ki
ciccire kwallayen sai ki
hada su guri daya ki kara ruwan kadan kisa sukari kadan
idan kina da firji kisa
a ciki idan kuma babu ki sak kankara akai ki ajiye shi narke
sai ki tsiyaya
ruwan zaki ga ya zama mai kauri kitib ki dinga sha zaki iya
hadawa da
yangudaddajin ma.
*▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒*
*✿・ HADIN NI'IMA 4・✿*
*dabino*
*madarar shanu*
*kanunfari gari*
*kirfa*
YADDA AKEYI
za'a sami dabino a shanya shi ya bushe sai a cire kwallon a
dakashi lukwi,
sannan a saka dakakkan garin janunfari a hada a kurfa guri
daya sai a dinga
zuba cokali uku ana hadawa da madara shanu ana sha safe
da yamma cokali
uku uku kullum tsahon sato guda.
❍ *HADIN NI'IMA 5* ❍
*garin idon zakara*
*garin tafarnuwa*
*ruwan khal*
*madarar shanu*
YANDA AKEYI
a sami garin idon zakara da garin tafarnuwa hada rabin
cokali a zuba a kofi a zuba ruwan khal karamin cokali a
hada da madarar shanu cikin kofi a hada a sha, akwai
saukar da ni'ima.
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
■ *HADIN NI'IMA 6* ■
_ruwan rake_
_zuma_
_garin tafarnuwa_
_garin kanunfari_
YANDA AKE HADAWA
a sami rake a nikashi a blander ko kuma a saka cikin tirmi
mai kyau a daka a
fitar da ruwan jiki, a zuba zuma mai kyau a kan ruwan
raken a saka garin
tafarnuwa kadan a zuba garin kanunfari rabin cokali a hada
a dinga sha akwai
saukar da ni'ima.
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
*ⓜ・ RUWAN NI'IMA 7・ⓜ*
*_madarar shanu_*
ruwan khal
*_zuma_*
ruwan kankana
YANDA AKE HADAWA
a sami kankana a nikata ko a yankata gutsi-gutsi a zuba
mata ruwa a barta ta
zagwanye a zuba a kofi a zuba ruwan khal da zuma a hada
da madarar shanu a dinga sha shima yana da kyau.
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒❯
*♜・ HADIN TUKUDI NA GARI・♜*
Gero
_kanunfari da citta da masoro_
hakin daka
*_sassaken kankana_*
dabino
*mazarkwaila*
sassaken baure
YANDA AKE YI
a sami gero a surfe shi a soya sam-sama sannan a dakashi
ko kuma akai nika yayi laushi sai a zuba a tirmi a saka
kanunfari garinsa da garin masoro da
garin sassaken kankana da garin dabino da dakakkiyar
mazarkwaila da sassaken baure a hadasu a daka lukwi a
shanya su a faranti ya bushe sai a dinga sha madara ko
nono ko yogot.