MIYASA INFECTION KEDA WAHALAR MAGANI?.

MIYASA INFECTION KEDA WAHALAR MAGANI?.

Da farko Lallai ya kamata ku gane cewa ‘infection’ yana da wuyar magani domin magani ne da sai an dauki lokaci ana yi kafin ya warke gaba daya, wanda inda son samu ne ku dauki lokaci kamar wata 6 a jere koma fiye shi ne za ki ga kin magance shi gaba daya, amma in za ki fara ki bari to lallai za ki dade kina magani ba ki magance shi gaba daya ba.

Kuma lallai wadda take da miji sai sun yi magani su biyu amma in ta sha magani ita kadai kamar ta yi a banza ne don suna kara saduwa da mijin za ta kara daukar ciwon.

A gwada daya daga cikin wadannan:

1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce, sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin bushewa da kaikayi.

2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection.

4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da bushewa da dodewar gaba.

5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.

6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni’ima.

7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.

8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni’ima da magance duk matasalolin sanyi.

9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba a kan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.

10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni’ima.

11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta na sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.

12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki dauki sala daya ki yi matsi da shi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki za ta yi hakan har tsawon kwana uku.
13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi. Insha Allahu idan akayi amfani da daya daga cikin wadannan zaa samu waraka. Duk wanda ya karanta wannan sakon yayi kokari sharing dinshi ga alumma domin yin haka zaizama kamar sadaqatul jariyah, Allah yabamu dacewa Amee.

Post a Comment

Previous Post Next Post