ICCEN KALGO KADAI YANA MAGANIN KUSAN DUKKAN MATSALOLIN MATA HARDA WASU MATSALOLIN MAZAN.

ICCEN KALGO KADAI YANA MAGANIN KUSAN DUKKAN MATSALOLIN MATA HARDA WASU MATSALOLIN MAZAN.

Bishiyar kalgo wata bishiya wadda Allah (S.W.A) ya albarkacheta da sunadarai masu karfin gaske wajen maganche wasu matsaloli dakuma yakar cututtuka daban daban daka iya tasiri a jikn dan adam.
Wannan bishiya anfi samuntane a kasashen africa da Asia inda shekaru da dama dasuke wuche ana sarrafa wannan bishiya domin nauikan magunguna kala kala.

Khalifa herbal medicine and marriage counseling munyi binchike domin kawo maku wasu faidoji dakuma yadda zaa bi domin sarrafa wannan bishiya mai Al barka.

MAGUNGUNA

(1) Ana zuba garin sassaken kalgo da sassaken baure cikin abinchi ko atafasasu da madara kokuma hakanan ajika garin da ruwa asha ko cikin shayidomin maganin ciwon sanyi ( gonorrhea ) da sauran cututtuka da ake iya dauka wajen saduwa.

(2) ana dafawa ko ajika saiwar ko ganyen ana shan ruwan domin maganin rikichewar alada , yawan bari, kokuma daukewar jinin alada.

(3) ana dafa saiwar kalgo ana shan ruwan domin yana maganin ciwon mara lokachin alada.

(4) ana dafa saiwar kalgo aba machen da ta haihu domin inganta lafiyarta.

(5) ana dafa ganyen kalgo ayi wanka da ruwan domin saukaka ciwon jiki.

(6) tauna ganyen kalgobayan andafa shi yana maganin ciwon hakora.

(7) ana dafa ganyen kalgo ashafa inda kai yake ciwo insha Allah zai daina.

(8) ana tafa ganyen kalgo ayi wanka dashi yana maganin masassara.

(9) ana shafa tokar kalgo a kirji domin maganin ciwon kirjin.

(10) ana amfani da garin sassaken kalgo domin maganin ciwon makoshi , ciwon hakori, ciwon kunne , ciwon ciki dakuma maganin kasala
da ciwon jiki.

(11) ana zuba garin sassaken kalgo ga rauni domin yayi saurin warkewa.

Wannan kadanne daga cikin amfanin kalgo domin neman shawarwari ko wasu magunguna zaku nememu ako da yaushe.

Post a Comment

Previous Post Next Post