TUSHE DA ASALIN HAKURI SAI MACE Tabbas mace tana da hakuri da juriya,

😭 😭 😭 😭 😭   

TUSHE DA ASALIN HAKURI SAI MACE
 Tabbas mace tana da hakuri da juriya,eh
Ina da hujjar fadin hakan. Idan mace ta dau ciki daga wata daya har zuwa hudu cikin wahala da laulayi take wata ma har ta haihu babu laifiya, amma jeki duba. Gaddafi (kai mai karatu dakai nake) idan yayi sati yayi yana malaria Sai
ya zama abin tausayi.

Idan tazo nakuda wata har Dan ya fita bata
hayyacin ta wata kuma ta karu Sai an mata
dinki,ga bakar azaba da budewar Kashi,duk
ita kadai,amma dubi malam inusa idan yaje
toilet yana basir .

Wata anan zata Sami hawan jini wata
buguwar jini amma duk da haka abinda zai
sanyaya mata Rai a wannan lokacin shine
kukan da jaririn zai yi na farko.

Ko kasan zafin da uwa take Sha a lokacin da
jaririn ta ta kama nononta na farko domin
sha?? Amma duk da wannan zafin hakan ba
zai hana ta bashi ba gudun kada yayi kukan
yunwa.

Da zarar da ya fara hakori,haka zai Kama kan
nonon ya ciza amma duk da haka murna
zata dinga yi tana nunawa jama'a kan dan
ta yayi hakori.

Tana cin abinci,barci take ko kuwa cikin taro
take haka zai yi fitsari ko kashi dole ta yanke
abinda take taje ta wanke mishi.

Ya girma yayi wayo haka zai dinga barar
mata da kaya yana mata barna amma ita ba
wannan bane damuwar ta,damuwar ta
shine kada yaje ya janyo abinda zai cutar
dashi.

Amma wai duk da haka mace itace abin
wulakantawa itace abin tozartawa,wani ma
uwar shi na fada yana fada idan baka
tausayawa mace ba ka mutunta to baka da
amfani.

Uba karfin shi yake baka amma ita uwa
lafiyar ta take baka Dan haka mace ta zarce
duk yadda kake tunani idan ka mutunta ta
wani zai mutunta taka uwar idan ka tozarta
wani zai tozarta taka.

Ya Allah duk wanda baya tausayawa mace
Allah ka hadashi da cinnaka mara tausayi
yayi ta gannawa Dan banza cizo😏
👇👇👇
Aisha Abdullah

Post a Comment

Previous Post Next Post