Ciwon Baya Mai Sauka Ƙafa Ne Matsalarka Kuma Ka Gaji Da Shan Magani?
Ciwon baya musamman mai sauka zuwa ƙafa, ciwo ne da ke da sabuba da dama. Sabuban sun haɗa da fashewa ko bullin faifan tsakanin ƙashin gadon baya, zaizayewar faifan tsakanin ƙashin gadon baya, amosanin gaɓar ƙashin gadon baya, tsukewar kwaroron laka da dai sauransu.
Saukar ciwon baya zuwa ƙafa na faruwa ne sakamakon danne ko shaƙe jijiyar laka a hanyarta ta zuwa ƙafa. Hakan kuma zai haifar da matsanancin ciwo, zogi, dindiris, jin yanayi kamar na shokin ɗin wutar lantarki, jin yanayi kamar ana tsitstsira allura, jin yanayi kamar tafiyar kiyashi a ƙafa da tafin sawu, duk waɗannan alamu ne na ciwon baya mai sauka.
Sau da yawa, ciwon na dawowa sabo ne bayan magani ya gama aikinsa. To yaushe ne za a daina sha ko shafa maganin kenan?
Domin fara bankwana da wannan ciwo ba tare da dogaro da sha ko shafa magani kullum ba, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.