BINCIKE | Lahanin da ke faruwa ga ƙwaƙwalwa bayan sa wa ƙwallon ƙafa kai

#BINCIKE | Lahanin da ke faruwa ga ƙwaƙwalwa bayan sa wa ƙwallon ƙafa kai

Hukumomin ƙwallon ƙafa a ƙasashen turai sun ce daga yanzu yara 'yan shekara 11 zuwa ƙasa ba za a riƙa koya musu buga ƙwallo da kai ba yayin ɗaukan horo. 
Ƙasashen turai da suka haɗa da Ingila, Sukotlan, da kuma Arewacin Ailan sun ɗauki matakin hana yara buga ƙwallo da kai ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar a Jami'ar Glasgow da ke Ingila, wanda aka wallafa sakamakon binciken a watan Oktoban 2019, inda binciken ya yi nuni da cewa tsoffin 'yan ƙwallon ƙafa na da ninki uku da rabi na haɗarin mutuwa daga cutukan ƙwaƙwalwa kamar larurar gigi, wato 'dementia' a turance.

Bugu da ƙari, binciken ya sake yin nuni da cewa tsoffin 'yan ƙwallon ƙafa sun fi mutuwa daga cutukan da ke kawo wa aikin ƙwaƙwalwa koma-baya, kuma suna da ƙarin ninki biyar na haɗarin mutuwa daga cutar Parkinson. 

[Cutar Parkinson matsalar motsi ce sakamakon raguwar ko ƙarewar sinadarin 'dorpamine' a ƙwaƙwalwa, kuma cutar ta fi shafar tsofi. Haka nan, ana gane alamunta na zahiri da bayyanar kyarma ko karkarwa a hannu ko yatsu da sauran sassan jiki, riƙewar gaɓɓai, nawa ko jinkirin motsi a ayyukan yau da kullum.]

Nauyin ƙwallon ƙafa ya kusa kai rabin kilogiram (0.5Kg) kuma masana sun ce ƙwallon za ta iya bugar kan ɗan wasa cikin sauri ko gudun da ya kai kilomita 128 cikin awa ɗaya (128km/h). A yayin da ƙwallo ta bugi kai cikin sauri zai haifar da jijjigawar ƙwaƙwalwa a cikin ƙoƙon kai wanda hakan ke haifar da kurjewa ga ƙwaƙwalwa.

Wani bincike da aka gudanar a Jami'ar British Columbia da ke Ingila a shekara ta 2018, ya nuna ƙaruwar sinadarin furotin a cikin jini wanda ke ƙaruwa bayan rauni ko lahani ga ƙwaƙwalwa.

Jawabin haɗin gwiwa da hukumomin ƙwallon ƙafan suka fitar ya ce an bai wa kociyoyi shawarar kada su riƙa koya wa yara sa wa ƙwallo kai lokacin ɗaukan horo. Yaran da aka hana su sa wa ƙwallo kai sun haɗa da 'yan firamare da 'yan shekara 11 zuwa ƙasa.

Amma hukumomin sun ce, yaran za su iya ci gaba da sa wa ƙwallo

Post a Comment

Previous Post Next Post