ME KASANI GAME DA YAYAN KUZBARA DA GANYEN TA (CORIANDER SEEDS AND LEAVES)

ME KASANI GAME DA YAYAN KUZBARA DA GANYEN TA (CORIANDER SEEDS AND LEAVES)

Kuzbara wani tsiro ne mai kamshi, mai arzikin antioxidant wanda ke da matukar amfani da yawa ta fannin dafa abinci da kuma fa'idodin kiwon lafiya.

Yana iya taimakawa wajen rage sukarin jini, yaƙar cututtukan Infections, da haɓaka ayyukan zuciya, ƙwaƙwalwa, fata, da inganta lafiyar narkewar abinci. 

Kuzbara tsiro ne da aka fi amfani da shi don karin dandanon girki a kasashen duniya.

Ya fito ne daga dangin shukar Coriandrum sativum kuma yana da alaƙa da Parsley, karas, da seleri.

Mutane da dama suna amfani da Kuzbara a cikin girke girke kamar miya da sauran su. 

Ana iya amfani da ganyen Kuzbara gabaɗaya, yayin da su kuma tsabar yayan ake amfani da su idan sun bushe ko kuma garin su.

Ga wasu daga cikin fa'idodin kiwon lafiya masu ban sha'awa na kuzbara.

1_ Tana iya taimakawa wajen rage sukarin jini.

Yawan sukari a cikin jini abu ne mai haɗari ga masu type 2 diebetes.

Ya'yan kuzbara da man kuzbara na iya taimakawa wajen rage sukarin jini. 

A takaice ma, mutanen da ke da karancin sukari a jini ko masu shan maganin ciwon sukari ya kamata su yi taka tsantsan wajen amfani da kuzbara saboda tana da tasiri sosai wajen rage sukarin jini.

Wani bincike da akayi da dabbobi ya nuna cewa tsaba na ya'yan kuzbarq suna rage sukarin jini ta hanyar haɓaka aikin enzyme wanda ke taimakawa wajen cire sukari daga jini.

Wani bincike da akayi a cikin berayen da ke da hawan jini an gano cewa kashi daya (20 mg per kg) na tsabar ya'yan kuzbara ya rage sukarin jini da kaso 4 mmol/L a cikin awanni 6.

A wani binciken mai kama da wannan an gano cewa anyi amfani adadin tsabar ya'yan kuzbara iri daya.
Ya taimaka wajen rage sukarin jini da haɓaka sakin insulin a cikin beraye masu dauke da ciwon sukari.

2_ Tana da wadata a cikin antioxidants masu inganta garkuwar jiki.

Kuzbara tana ba da antioxidants da yawa, waɗanda ke bada kariya daga lalacewar kwayoyin halitta wanda free radicals ke haifarwa.

An gano cewa antioxidants dake cikin ta yana taimakawa wajen yakar kumburi a cikin jiki.

Wadannan sinadaran sun haɗa da terpinene, quercetin, da tocopherols, waɗanda suke dauke da anticancer, immune boosting, da kuma tasirin neuroprotective, bisa ga gwaji da nazarin dabbobi.

3_ Zata iya amfani wajen inganta lafiyar zuciya

A wani nazari na dabbobi da gwajin test-tube sun nuna cewa kuzbara na iya rage haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya, irin su hawan jini da matakin mummunan cholesterol. 

Kuzbara ya bayyana cewa tana aiki a matsayin diuretic, dake taimakawa jikin mu wajen fitar da sodium mai yawa da ruwa. Wannan na iya taimakawa waje rage hawan jini.

Wasu bincike sun nuna cewa kuzbara na iya taimakawa wajen rage cholesterol. 

Ɗaya daga cikin binciken ya gano cewa berayen da aka bawa tsabar ya'yan kuzbara sun sami raguwa sosai a cikin mummunan cholesterol da samun karuwar cholesterol mai kyau.

4_ Zata iya bada kariya ga lafiyar kwakwalwa. 

Mafi yawancin cututtukan kwakwalwa, wanda suka hada da Parkinson's, Alzheimer's, da multiple sclerosis, suna da alaƙa da kumburi.

Duba da cewa kuzbara nada anti-inflammatory properties zata iya bada kariya akan wadannan cututtukan.

Wani bincike ya nuna cewa ganyen Kuzbara yana inganta ƙwaƙwalwar ajiya, wannan ya nuna cewa tsiron na da amfani akan cutar Alzheimer.

5_ YANA IYA INGANTA NARKEWAR ABINCI. 

Kuzbara tana rage alamomin na rashin jin dadin narkewar abinci kamar kumburi da rashin jin daɗi da mutanen da ke da irritable bowel syndrome ke fuskanta.

Sannan kuma tana iya haɓaka sha'awar cin abinci a tsakanin wasu mutanen.

6_ Zata iya yaƙar cututtukan Infections. 

Kuzbara tana ƙunshe da antimicrobial compound waɗanda zasu iya taimakawa wajen yaƙar wasu cututtukan Infections da cututtuka dake samuwa ta abinci (foodborne illness)

Dodecenal, wani sinadari a cikin kuzbara, na iya yaƙar ƙwayoyin cutar bacteria kamar Salmonella, wanda zai iya haifar da guba ta abinci mai barazana ga rayuwa.

Bugu da ƙari, wani binciken test-tube ya nuna cewa tsabar yayan kuzbara na daya daga cikin sinadarin girki na mutanen india waɗanda yake iya yaƙar ƙwayoyin cutar bacteria da ke da alhakin cututtukan urinary tract (UTIs).

7_ Zata iya bada kariya ga fata

Kuzbara na ƙunshe da  antioxidants waɗanda zasu iya kare fata daga tsufa da lalacewa sanadin rana. Hakanan tana iya taimakawa wajen magance dabbare dabbare akan fata.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post