Maimaituwar Gocewar Kafaɗa Ce Matsalarka?

Maimaituwar Gocewar Kafaɗa Ce Matsalarka?

Gaɓar kafaɗa ita ce gaɓa mafi raunin kafuwa a cikin gaɓoɓin jiki. Haka ne ya sa take da saurin gocewa tare da maimaituwar gacewar. 

Gocewar gaɓar kafaɗa na iya afkuwa daga bugu, faɗuwa, faɗowa, wasanni ko kuma ayyukan sana'o'i. 
Maimaituwar gocewar gaɓar kafaɗa abu ne da ke sa gaɓar cikin rashin tabbas. 

Gyara gocewar kafaɗa aiki ne da ke buƙatar ƙwarewa domin samun mafi kyawun waraka tare da kauce wa haɗarin maimaituwar gocewa ko kuma janyo mummunan lahani ga muhimman sassan gaɓa. Sau da yawa, rashin ƙwarewa na iya haddasa mummunan lahani ga sassan gaɓar kamar tantanai, gurunguntsi ko kuma jijiyoyin jini da jijiyoyin laka da ke kusa da gaɓar.

Maimaituwar gocewar kafaɗa matsala ce da za a iya magance ta ko rage afkuwar ta akai-akai. 

Idan kana / kina fama da maimaituwar gocewar kafaɗa, tuntuɓi likitan fisiyo domin fara bankwana da matsalar a yau.

©Physiotherapy Hausa

Post a Comment

Previous Post Next Post