WANI JINKIRIN ALKHAIRI NE 'GA "Ya" MACE !!!•

WANI JINKIRIN ALKHAIRI NE 'GA "Ya" MACE !!!
Sau da yawa za ka samu mace ta kai wani mataki wanda ya kamata a ce ta yi aure amma har yanzu ba ta yi ba, age-mates ďinta sun yi aure wasu ma har da 'yaƴa, ita kuma qin yin auren ba daga gare ta bane, ita tana so, sai dai kuma har yanzu Allah be kawo mata mijin aure ba. 'Yar uwa wannan ba komai bane illa jarabawa daga Allah Mabuwayi, mai yiyuwa ya jarrabe ki ne domin Ya ga yadda za ki yi, idan kika yi hakuri kuma kika mayar da Al'amuranki ga Allah, sai ki ga Ya kawo maki miji adali mai addini da kyawawan dabi'u da dukkan siffofin da mace za ta bukata a wajen namiji ta hanyar da ba ki yi tsammani ba 'yar uwa. 

Allah Shi ne Ya yi alkawarin zai jarrabi muminai a duniya da jarabawa iri-iri, kuma Ya ce Lallai a yi bushara ga masu hakuri. 'Yar uwa wani irin babban rabo kike tunani Allah Ya tanadar maki idan kika kasance cikin masu hakuri. 

Hakurin shi ne a kowane lokaci ki dinga jin Allah Yana son ki, kuma Yana sane da halin da kike ciki, kada ki kai kukanSa wajen bayinSa, kuma ki kasance mai kiyaye iyakokinSa, ki Tsare ganinki, jinki daga haramun kuma ki kiyaye al'aurarki, ki kare mutuncin kanki kuma kada ki tozartar da tarbiyyar da su Abba da Umma suka ba ki, kada ki aikata abin da za su yi da-na-sanin zuwanki duniya, Sannan kada ki aikata abin da zai zama abin gorantawa ga Qannenki, 'yaƴanki da dukkan wanda yake da alaqa ta jini da ke! Ki bar tarihi mai kyau ko don gaba, kuma ki ji tsoron Allah ki dinga dubin abin da kike aikatawa don gobe. 
Da yawa daga cikin 'Yan mata kamilallu sun rasa kimarsu, inda suke tunanin mai yiyuwa sanya wadataccen hijabi da Niqabi ne ya jawo masu jinkirin aure, sai suka koma yin shiga irin ta tsiraici da bayyana adonsu wai da sunan samun mijin aure. 'Yar uwa Wallahi arhar ta yi yawa, meyasa sai kin tallata kanki za ki samu mai aure, kin ta6a ganin wani abu mai daraja ana tallata shi, duk wani abu mai daraja rufe shi ake kuma a adana shi a mafi dacewar guri, shin a tunaninki tsinuwar Allah da

Post a Comment

Previous Post Next Post