TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN TAYI:Amsoshin game da game da tambayoyin akan daukan ciki, renon ciki, da kuma bayan haihuwa.1. YAYA ZAN GANE INA DA CIKI:

TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN TAYI:

Amsoshin game da game da tambayoyin akan daukan ciki, renon ciki, da kuma bayan haihuwa.

1. YAYA ZAN GANE INA DA CIKI:

Alamomi da yanayin samun ciki ya banbanta daga mace – zuwa mace, daya daga cikin alamomina samun ciki shine ;rashin ganin jinin karshen wata, wasu matan zasu ga chanji kadan ko ma babu chanji a farko, daga nan wassu alamomi zasu baiyana.

Alamomin sun hada da gajiya, yawan fitsari, tashin zuciya, girman nono, da kuma yawna kwadayi mafita, shine ayi gwajin ciki.

2. INA TSAMMANIN INA DA CIKI YAYA ZANYI?

In kina tsammanin kina da ciki ki fada ma ma’aikacin lafiya (likita ko ingozuma) da wur-wuri. Akwai abubuwa da yakamata kisani akan ciki juna (biyu). Kamar zaben wanda zai kula da ke lokacin goyon ciki da kuma yada zaki gano damuwowi lokacin goyon ciki.

Ya kamata ki fahinta cewa kula da lafiya da wuri akan lokaci yana da mahimmanci ga lafiyanki. Dan haka yafi muhimmanci ki nemi mai’akacin lafiya da wur-wuri dan kula da juna biyun (ciki) ki.
Zuwa akan lokaci, a a’ida wurin awu akuma asibiti yana da amfani make da abinda yak e cikin ciki (yaro) .

3. MI ZNAYI TSAMMANI ALOKACIN GOYON CIKI?

Ako da yaushe renon ciki yanayine na chanje- chanje lafiya dayawan mata duk da haka wasu cuttattuka zasu bullo a lokacin goyon ciki.
Zuwa awu zai taimaka wajen gano damuwa da kuma magan ceta kafin ta zama babba.
Wannan sun hada;
Hawan jinni
Ciwon suga
Yawan amai
Karanci jinni
Rashin zagawan jinni
Ciwon koda
Ciwon kunkumi
Kaikayi da ciwon jiki
Kyama
4. INA YA KAMATA NAJE IN INA DA CIKI?
Ki tafi asibiti ko shakatafi mafi kusa dake dan shigar da sanan ki cikin rigistar masu juna biyu dan kulawa.
5. SABODA MI ZANJE AWU ?
Zuwa wajen awu yana da amfani a gareki da kuma yaron da kike dauke dashi
matan da suke zuwa wajen akan lokaci sukan samu:
Lafiyayen yaro
Basu haihuwan yaron da baiyi kwari ba
Sukan samu kulawa akan cututtuka tun kafin su zama damuwa a garesu da yaron su
6. YAUSHE YA KAMATA NAJE AWU.?
Ya kamata ki je wajen likita, mai aikin jinya ko kuma ingozuma daga zarar kin. fahimci kina da ciki (juna biyu), yana da muhimmanci ki fara zuwa awu watannun .
7. WASSU MUHAMMAN BAYANE ZAN TANANA LOKACIN ZUWA AWUN FARKO?
Zuwanki na farko zai baki daman a saki jerin masu zuwa awu zaki ba ma ingozuman ki bayanai muhimmai daga nan zata saki jerin wanda za’ana kulawa dasu tsawonlokacin goyon ciki awannan asibitin ko shaka tafin.
In daga baya kika yanke shawaran haihuwa a wani asibiti daban da wanda kike awu, sai ki tattauna da ma’aikatan lafiya.
8. SAU NAWA YA KAMATA NAJE AWU.?
Likitan ki zai baki tsare –tsaren zuwan ki awu tsawon lokacin goyon ciki.
Masana sunce kije wajen likita.:
Sau daya a wata bayan sati hudu (4) sati (8) ishirin da takwas
Sau biyu a wata da satina ashirin da takwas (28) din sati 36.
Duk sati daga sati na talatin da shida (36) har zuwa haihuwa.
- In kinfi shekara 35 ko goyon cikin yana da matsala to zaki ga likata akai akai
9. MI YAKE FARUWA LOKACIN AWUN?
Lokacin awun farko kiyi tsammanin :-
Tambaya akan tarihin lafiyan ki wanda ya hada da cutattuka, tiyata ko goyon cikin daya wuce
Tambaya akan tarihin lafiyan zuriyar ki
Gwajin lafiyan jikin wanda ya hada kumkumi
Gwajin jinni, da tsayi da dauyi
Lissafin yawan kwana kin cikin
Amsar tambayoyi.
A awun farko kiyi tambaya ki kuma tattauna akan muhimman abubuwa da suka shafi juna biyu. Ki kuma tambaya ta yadda zaki zauna cikin koshin lafiya, awun da zasu biyo baya kuma tambayoyin zasu zanto kadan.
Likitan ki zai binciki lafiyan ki ya kuma tabbatar yaron da yake cikin ki yana girma yanda ya kamata.
A bubuwan da aka fiyi lokacin awu sun hada da:-
Gwajin hawan jinni
Gwajin nauyi
Gwajin tsayin ko girma ciki dan gane girman yaron ciki
Dubawan bugun zuciyan yaron dake cikin ciki
Tsawon lokacin ciki (juna biyu) akwai gwaje- gwajen da zaki nayi.
Akan gwaje- gwajen da ake so duk mace mai ciki tayi, sun hada da gwajen jinni dan giare yawan sa, rukunisa, dakuma halittan sa, cutan kanjamau da kuma za’ayi su dangane da shekaru, tarihin cutattukan ki ko na zuriyan ki ko kuma gwaje-gwajen da ki ka gudanar.
10. MI YA KAMATA NA CI LOKACIN GOYON CIKI?
Ire- tren abincin da suke da amfani lokacin goyon ciki sun hada da:-
Grains, kamar, gurasa alkama tuwo
Ya’yan itatuwa; cin su kafin sarrafawa da kuma sarrafeffe wanda kashin dari (100) ba wani
Kayan lambu alaiyafo, kanji, karas da sauransu.
Masu gina jiki nama, naman kaza, halittan ruwa (kifi), wake kwai, awara, da sauran su
Shanu: nono, madara da kuma abubuwan da akayi da madaran
11. WANI IRIN ABINCI YA KAMATA MAI CIKI TACI A SATUKAN FARKO SAMUN CIKIN TA?
Mace mai ciki yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan mar-mari (lemo, ayaba). Masu gina jikin sun hada da; kwai, kifi, nama, dodon kwodi madara da dai sauran su, mace mai ciki ta guji ire- iren abincin da zaisa ta tashin zuciya.
12. MI YASA ZAN CHANZA NAU’IN ABINCI NA IN I NADA CIKI?
Abincin da yake dauke da sinadarai abinci duka yana samar sinadaren, da ake nemana wajen tafiyan girma da kuma rayuwan sashin jikin da kuma naman jikin halittan dake cikin ciki ta hanyan kare shi daga cutar kwakwalwa da kuma ‘kashin baya lokacin haihuwa.
13. WANI HANYA ZANBI DON ZAMA CIKIN KOSHIN LAFIYA LOKACIN GOYON CIKI?
Yana da muhimmancin zama ciki koshin lafiya lokacin rainon ciki ta hanyan.
Cin abinci mai dauke da sinadaren da jiki yake bukata
Motsa jiki
Yana da muhimmanci ku tattauna akan motsa jiki da likitan ki ko wani ma’aikacin lafiya na asibitin da kike zuwa kafin fara kowani nau’in na motsa jiki. Mafiya yawan lokuta motsa jiki ga mai ciki yana da muhimmanci. In kama mai lafiyan kabbai kafin samun ciki haka ake tsammanin ka zama cikin lafiya ko lokacin goyon ciki. Likitan ki zai shawarce ki kara kokarin dan zama cikin kashin lafiyan abbai makawan bazai zamo matsalaba ga lafiyan kid a kuma na jarinn da kike dauke das hi
14. MINENE MUHIMMANCIN MOTSA JIKI LOKACIN GOYON CIKI?
Ga kadan daga ciki:-
- yana taimako wajen rage ciwon baya, tashin zuciya, kumburan kafa da kuma kunburin Jiki.deep
- zai taimaka wajen kare ko lura da ciwon suga na lokacin goyon ciki
-zai tamaka wajen Karin karfi
- Zai taiamaka wajen bunkasa yanayi
- Yana taimakon karfin jiki, jinya da kuma lafiyan jiki.
- Yana taimakon ki wajen yin barci mai dadi
- Yawan ta yin motsa jiki yana taimakawa lokacin goyon ciki kuma yana taimakawa lokacin nakuda, haihuwa da kuma lokacin biki.
15. WASSU IRIN CHANJI SUKE BAYYANA A JIKI LOKACIN GOYON CIKI WANDA ZAI CHANZA YANAYIN MOTSA JIKI.?
Jikin ki yana shiga yanayin chanje –chanje lokacin goyon ciki, daga lafiya, tunani da kuma lafiyan gobobi.
16. WASSU HANYOYIN ZAMBI WAJEN MOTSA JIKI LOKACIN GOYON CIKI?
Akwai hanyoyin kadan da mace mai ciki ya kamata ta san dasu lokacin motsa jiki.
Saka kayan da suke matse jiki kamar rigar mama, da kuma daure ciki dan kar aji ba dadi
Akiyaye tsayiwa guri daya lokacin motsa jikin dan kar jinni ya karu a kafa.
A kiyaye kwanciya a gadon bayan ciki yana tare da jijiyoyinasu mai jinni zuwa zuciya, hakan yana rage zuwan abinci ga yaron da ke cikin ciki
17. AKWAI YANAYIN DA ZAI BAIYANA A LOKACIN GOYON CIKI DA BAIKA MATA A MOTSA JIKI BA?
Akwai, bai kamata ki motsa jiki lokacin goyon ciki ba in likita ya taba gwada ki da daya daga wandan nan cutattuka:-
Gaggarumin ciwon zuciya
Ciwon huhu
Rashin lafiyan mahaifa
Rashin tsayinwar jinni fiye da wata biyu ko uku.
Nakuda kafin lokacin haifuwa
Tagewan naman cinya
Idan kuma an gwada ki, ko kin taba ganin daya daga cikin wandan nan cutattuka to ki nemi izini a wurin likitan ki kafin ki motsa jikim, sun hada :-
- karanjin jim
- Chan-chanzawan bugun zuciya
- yawan haki
- raguwan nauyi
- shan maganin dan rayuwa
- Tsiran nama acikin maihafa lokacin goyon ciki
Rashin kwarin kashi
Shaye –shayen kamar (taba giya)
Kunburi, ciwo da kuma tara jinni a gabobi.
Daukan lokaci cikin nakudan
Rashin juya wan ciki
Fitan rowan mahaifa
18. I NA SHAN GIYA KUMA INA DA CIKI IN BARI?
Shangiya lokacin goyon ciki zai iya illatar da yaron da yake cikin ciki. Giya zai iya shiga cikin yaron daga mahaifiya ta cikin jini kuma hakan zai iya lalata kwayoyin halittan yaron yayin da yaron ya fara girma a cikin ciki. Kuma yana bata kwakwalwan yaron. Dan haka aguji giya matsawar iyawa lokacin goyon ciki.
19. WANI IRIN MAGANI YAKAMATA INA SHA?
Maganin da ake bayarwa lokacin awu sune ya kamata ki sha lokacin goyon ciki. Amma ya kamata ki tambayi shawar likitan ki kafin shan kowani irin magani.
Bai kama ki sha kowani irin maganin ba in kina da ciki sai kin samu izini daga likita.
20s. WASSU IRIN GWAJE –GWAJE YA KAMATA NA YI LOKACIN GOYON CIKI?
Sun hada dai:-
- Gwajin fitari
- Gwajin jini dan chutattuka kamar su; kanjamau, mageduwa, ciwon hanta matakin farko da na biyu.
- Gwajin dan gane yawan jini .
- Tantance yawan suga
- Daukan hoton yaro.
21. MI YASA MACE MAI CIKI ZATA JE DAUKAN HOTON CIKI?
Dalili shine:-
- Daukan hoton ciki yana taimakawa wajen gane lafiyan yaron da yake cikin ciki Kuma ana gane jinsin  macene ko namijine a cikin ciki.
22. NA SHAGALTU DA AIYUKA DA HAR SUN HANANI ZUWA AWU YAYA ZANYI?
Lafiyan ki da na yaron dake cikin ciki ki yana da muhimmanci, ya kama ta ki ware lokacin zuwa wajen awu a takaice sau hudu (4) a keso. In kuma kina ga baza ki samu daman zuwa awun ba ki kira asibitin awaya ki gaya masu, zasu taimaka maki su sake baki lokacin zuwa kuma.
23. INA AMFANI DA TSOFI A GIDA LOKACIN HAIHUWA MI ZAISA NAJE ASIBITI?
Ma’aikatan lafiya zasu kula da ke ta fuskoki da dama fiye da haihuwa agida. Ma’aikatan lafiya suna kulawa da mai ciki da lafiya suna kuma bata muhimman bayane akan goyon ciki ta hanyan da zaki kare kan ki dana dan da kike dauke dashi. Misali zasu maki hoton yaron, hawa da sauakan suga, hawan jini, girman yaron, bugun zuciyan yaron, da kuma girman jaririn, da kuma Karin wassu abubuwan.
Kumadu zasu taimaka maki wajen gano minene damuwan ki bayan haka su baki kulawa na musamman wanda yahada da na gaggawa da kuma masu matsala.
24. WASSU IRIN ALAMOMI NE NA TSORITARWA LOKACIN GOYON CIKI?
Idan daya daga cikin wandannan suka baiyana to a dauki mai cikin zuwa asibiti mafi kusa dan tseratar da rayuwan ta, alamomin sun hada da:-
Zuban jinni daga mara.
Cizon harshe da yawan mika.
Ciwon kai da rashin gani.
Zazzabi da ciwon jiki.
Ciwon ciki
.Rashinko yawan numfashi.
Yawan ciwo.
Kumburin kafa, yatsu, da kuma fuska.
25.MI YA KAMA NAYI IN NAGA ALAMOMI MASU TSORITARWA?
Karki firgita ko kiji tsoro, kinemi taimako dan zuwa asibiti mafi kusa da ke.
26. YAYA ZAN SHIRYA MA HAIHUWA?
Lokacin awun ciki kiyi magana da likitan ki / ingozuman ki akan na’kuda da kuma hanyoyin da zakibi ki haihu. Zaki iya rubuta wa a matsayin tsarin haihuwa, inda zaki haifi danki, wazai karbi haihuwan, mi yakamata ki tanada lokacin haihuwa.
Da dai ki zama mai sassauci, ba wani haihu ko nakuda a za’a gane cikin sauki ki sallamar da kanki da duk canje-canjen da zai bullo miki a ko wani lokaci. Kuma ki shirya ma haihuwar jaririn ki bayan yanda kika shirya a baya yana iya zuwa ba yadda kike tsammani ba.
Idan abin gaggawa ya taso likitan ki shine ya dace ya kula da lafiyan ki dana yaronda kike dauke dashi cikin sauki, zaki iya bada shawara amma a takaice.
27. WASSU MATSALOLIN NE MAI CIKI ZATA FUSKANTA DA ZAI SAKA A MATA TIYATA BA TARE DA TA HAIHU DA KANTA BA?
Tiyata; a na yinsa ga mace mai ciki in kunkumin ta ya zama karami ko yaron ya zama kato da yafi karfin ya fito ta maranta ko yaron ya kai-kaita a cikin ciki.
28. WASSU MATSALOLINE SUKE DAUKE DA KWANCIYAN CIKI?
Kwanciyan ciki kafin samun sa da kuma bayan samun sa yana faruwa. Ko da yake in ciki ya kwanta kafin samun yaro ana kiran yanayin na farko (previa) za’a iya ganewa ta hanyan daukan hoton cikin kuma zai iya samar da zuban ciki daga karshen lokacin goyon ciki, likita zai maki bayani akan yanda zakiyi idan haka ya faru.
29. MI ZANYI TSAMMANI LOKACIN NAKUDA?
Alamomin nakuda sun bambamta daga mace mai ciki zuwa mace mai ciki. Wadannan sune alamomin nakuda:-
Budewan mara.
Fitan ruwa mai hade da jini mai yauki daga mara
Fitan ruwa marar yauki daga mara.
Fitan ruwa mai yauki ba tare da jinni ba
30. ME AKE NUFI DA TAZARAR HAIHUWAN IYALI?
Tazarar haihuwa; daga ma’anan sa shine yanke shawara akan yawa da kuma tazaran ‘ya’ya ta hanyan amfani da abubuwan hana daukan ciki, kamar su guje ma saduwa, tsarin yanayi ko ta hanyan kiyaye jinin haila.
31. WAYE ZAI IYA TAZARAR HAIHUWA?
Duk wanda yake da sha’awa zai iya yin tazarar haihuwa.
32. TA YAYA ZANYI TAZARAR HAIHUWA?
Kije a sibiti da kika yarda dashi dan samun bayani akan tazarar haihuwa sai ki zabi sonki cikin su.
33. WAYA KAMATA NAJE GUNSA DON TAZARAR HAIHUWA?
Kije wajen likita ko Ingozoma domin tazarar haihuwa.
34. A INA ZAN SAMU TAZARAR HAIHUWA?
Kije asibi mai kyau mafi kusa dake.
35. WASU IRIN HANYOYIN TAZARSAR HAIHUWA NE AKWAI KAFIN HAIHUWA DA KUMA BAYAN HAIHUWA?
Guje ma saduwa, kororon roba na mata, kwayan magani da kiyaye lokacin haila
36. TA YAYA ZAN KULA DA JARIRI?
Ki saka sunan ki a jerin masu rainon yaro a bayan haihuwa a asibiti mafi kusa dake, kuma kina zuwa tattaunawa kuma ki kula da duk shawarwarin da aka baki a lokacin tattaunawar.
37. MAI YASA ZANJE ASIBIT BAYAN NA HAIHU A GIDA?
Zuwa asibiti bayan haihuwa yana da muhimmanci a tsakanin awa ashirin da hudu (24hrs) ga duk wanda ta haihu a gida da kuma sati daya bayan haihuwa.
Likita yana duba lafiya da rayuwar yaro, halamun cututtuka akan lafiyan jariri ana gane su da wuri wuri kuma a magance su.
38. YA KAMATA LIKITA YA DUBA NI BAYAN HAIHUWA?
Ya kamata likita ya duba lafiyan ki bayan haihuwa don tabbatar da samun karfin jiki da kwari bayan haihuwa.
39. WASSU IRIN MATSALOLI YA KAMATA NA KIYAYE MA JARIRI NA?
Wadannan sune matsalolin daya kamata ki kiyaye da kuma kula ma jariri;
Daina shan Mama (nono) tun haihuwa ko tsayawa da sha.
Yawan numfashin sau sittin (60) ko fiye da haka cikin dakika daya (1sec)
Wahala wajen yin numfashi.
Zafin jiki da sama da kashi talatin da biyar da digo biyar 35.5 (Zazzabi)
Zafin jiki da kasa da kasha talatin da biyar da digo biyar 35.5
Rashin kuzari koa an motsa jariri (Rashin karfi)
40. MAI YA KAMATA NAYI INNA GA IRIN MADANCAN ALAMOMIN?
Karki tsorita, ki nai mi taimako, kikai jaririnki asibiti mafi kusa dake.
41. INA ZANJE DON KULA DA JARIRI?
A koda yaushe yana da muhimmanci zuwa asibiti ko sha katafi.
42. BAI KYAUTUWA A BAMA JARIRI RUWA?
Ba’aso a bama jariri ruwa, Jariri yana samun ruwa daga (nono) mama, (nono yana da kashi 90% ruwa) ruwa da wani abu ba nono ba ana kallonsa bai da kyau ga jariri, zai iya sashi gudawa.
43. IN NA YANKE SHAWARA KARNA SHAYAR DA JARIRINA DA MAMA (NONO) WACE HANYA ZANBI?
Sai dai in uwa tana da wani rashin lafiya na musamman shayar da jariri shine mafi kyau. Amma idan da wani dalili irin abincin jariri ya kyautu ayi amfani dashi ta yanda ya dace.
44. ME AKE NUFI DA SHAYARWA DA MAMA (NONO) KADAI GA JARIRI?
Shyarawa da Mama (Nono) kawai yana nufin uwa ta shayar da jariri da nono kawai. Duk wani ruwa ko abinci kar a bayar ko ruwa ma ba’a so. Amma maganin yara na ruwa za’a iya bama jariri.
45. MENENE MUHIMMANCI BAMA JARIRI IYA MAMA (NONO)?
Rowan Mama (Nono) yana da muhimmanci ga mace da kuma jaririnta. Shi mama (nono) yana dauke da sinadarai wadanda jariri yake bukata har tsawon wata shida (6month).
46. TSAWON WANI LOKACI MACE YA KAMATA TA SHAYAR DA JARIRIN TA?
Jarirai ya kamata a shayar dasu da ruwan mama (nono) tsawon wata shida (6 mouths) saboda a samu kyakykyawan girma da ci gaba cikin koshin lafiya. Daga baya a fara basu abinci mai gina jiki. Jarirai suna bukatar abinci mai gina jiki na musamman, Kuma a ci gaba da basu mama (nono) zuwa tsawon shekara biyu (2) ko fiye da haka.
47. ME AKE NUFI DA RUWAN NONO NA FARKO DA ZARAR AN HAIHU?
Shine ruwa nono na farko da zai fara fitowa daga mama (nono) mace bayan haihuwa. Nono ne na musamman launin yalo ko kalar lemo mai kauri da danko. Yana da karancin mai amma yana da sinadarin Karin karfi dana gina jiki.
48. MINENE MUHIMMANCIN NONO ( MAMA) NA FARKO?
Yana da tarin sinadarai masu bada kariya ma jiki wanda suke taimako wajen Kare lafiyan jariri. Kuma yan taimakawa jarirai wajen Karin lafiya. Kuma yana taimakawa wajen kare shawara ga jariri.
49. SHIN YA KAMATA KAR A BADA NONO FARKO GA JARIRI?
A’a Bai kamata ba dacewa yayi ya zamto abinci farko ma jariri.
50. YAKAMA MACE MARAR LAFIYA TA HAYAR DA JARIRI?
Ya kamata, matsawar mace mai shayarwa zata iya, sai dai in likita ya bada shawara kar ta shayar.
51. ADDININA YA HANANI HAIHUWA A ASIBITI TO YAYA ZANYI?
Ma’aikatan lafiya sun samu horaswa akan renon ciki da kula da jarirai, suna fahinta yanayi akan ciki da kike daukan shi kuma suna bada taimako wajen haihuwa da kuma dakile duk wata matsa da yake da alaka da goyon ciki da kuma haihuwa.
52. INA DA CUTAR KANJAMAU, TAYAYA ZAN KIYAYE CIKIN DA NAKE DASHI.?
Kije asibiti da wuri dan dubanwa kuma kulada daukan cutar daga uwa zuwa ga jariri.
53. YA KAMATA NAZO DA ABOKIN MAZANA ASIBITI? YA KAMATA NA ZODA DANGINA KO ABOKINA ASIBITI?
Ya kamata, ana maraba da duk wanda zaki zo dashi inhar hankalinki ya kwanta dashi wajen sanin sirrinki ko in yana taimakamiki da goyon ciki.
54. INA FAMA DA TSORO DA FARGABA TA YAYA ZUWA AWU ZAI TAIMAKA?
Ba ke ka dai bane acikin haka. Tsoro, fargaba ko duk wani nau’in damuwa baida dadi. Mata masu juna biyu suna fama da haka a lokacin goyon ciki.
Zuwa awu zai taimaka wajen samun sauki, shawarwari da kuma karfafawa akan duk wani damuwa. Dan haka ki tautauna da ma’aikacin lafiya akan haka.
55. MI NENE SHIRYE –SHIRYEN HAIHUWA DA KUMA MATSOLOLIN SHIRIN?
Tanadan abunda yake tattare da ciki dan samun ilimi akan awu mai ciki da kuma bayan ta haihu. Yana bada daman shiryawa da yanke shawara akan haihuwa ga ita mace mai ciki da kuma danginta.
56. MIYA KAMATA MIJINA YA SANI LOKACIN GOYON CIKI?
Da farko ki gaya masa da zaran kin fara ganin alamomin samun ciki, ki gaya masa bayani akan awu kuma ki sashi gami da bashi bayanai akan goyon ciki.
57.MINENE ABU MAI MUHIMMANCI DA MIJI ZAIYI LOKACIN GOYON CIKI DA KUMA BAYAN HAIHUWA?
Miji ya kamata ya taimaki matarsa da kudi dan zuwa awu, ya kuma karfafeta da magana mai dadi, ya kuma rakata zuwa awu, ya kuma tabbata tasha maganin da aka bata a wajen awu. Ya kamata miji yana tarun kudi dan jiran ranar haihuwar matansa.
58.SHIN YA KAMATA MIJI YA SADU (JIMA’I) DA MACE MAI CIKI?
Zai iya yana ma da amfani saduwa da mace mai ciki daga farko har karshen cikin lokacin haihuwa sai in likita ya hana saboda wassu dalilai.
59.KAMAR SAU NAWA MACE MAI CIKI YA KAMATA TA SADU (JIMA’I) DA MIJIN TA?
Duk yawan da take so, ba’a kaiyade ba yawan da mace mai ciki zata sadu (jima’i) da mijin taba.
60. MI YASA WASSU MATA SUKE DA DAMENMEN CIKI WASSU KUMA SAKAKKE?
Mata masu damenmen ciki mafiya yawan lokaci suna da yanayin bayan su a dame da farko fiye da mata masu sakakken ciki.
61. TSAWON WANI LOKACI MACE MAI SHAYARWA ZATA JIRA KAFIN TA FARA SADUWA (JIMA’I) DA MIJIN TA?
Da zarar ta daina ganin jinin biki, ko gurin da aka mata tiyata ya warke ko kuma taji tana son yi. Ya kan dauki kamar sati biyu ga macen da ta haihu da kanta.
62. YANA DA AMFANI NA SADU (JIMA’I) DA MIJIN NA LOKACIN GOYON CIKI?
Yana da muhimmanci amma ki nemi shawaran likita.
63. YAUSHE MIJI YA KAMATA YA DAINA SHAN MAMA (NONO) MATAR SA MAI CIKI?
Miji zai iya shan mama (nono) mace mai ciki amma ya kamata yana lura dan yawan shan zai sa sinadarin da yake taimakawa wajan nakuda yazo, hakan kuma zai sa haihuwan yaro maras kwari wanda watanninsa basu cikaba.
64. MACE ZATA IYA SAKA KARAMIN WANDO BAYAN HAIHUWA?
Sosai makuwa, ai kamar ta rufe al’aurar tane ma.
65. KAMAR SU MI DA MI MIJI YA KAMATA YA SAYAWA MATARSA KAFIN TA HAIHU?
Miji ya kamata ya tuntubi ingozuma dangane da mi da mi ya kamata ya saya. Wasu da cikin abubuwa sun hada dawa audugan kanti, tagaddan goge majina, mayin yara, sabulun wanka na yaro dana uwa da kuma zannuwa.
66. MINENE YAWAN JININDA MAI CIKI YA ZAMTO TANA DASHI?
Kamar kashai talatin da biyu(32%) cikin dari (100).


Post a Comment

Previous Post Next Post