RAYUWA KENAN
wata rana sai fada ya hadasu yabita hanya yasa bulala ya zaneta tayi kuka sosai ta share hawayanta,
bayan kammala primary ta tafi zuwa secondy sai akaimata aure , shikuma yaci gaba da karatunsa har jami a , bayan yagama jami a ya dade bayyi aure ba domin fafutikar neman aiki ,bayan yasami aiki sai yayi tunanin yayi aure ,
wata rana yaje wucewa ta wata islamiyya sai yaga wata yarinya ya yaba da hankalinta nutsuwarta da tarbiyar , sai yake ganin yakamata ya aureta ,
alokacin antashi daga makaranta bayyi wata wata ba yagabatar da kansa agareta kuma ta amsa kuma ta kwatanta masa gidansu,
ya dade yana zuwa gidansu budurwar tasa ,
watarana ya gayawa masoyiyarsa ta gayawa mahaifiyarta zai shiga sugaisa, bayan ta gayawa mahaifiyar tatane tadawo domin tayimasa iso,
suka shiga gida kowa na dan murmushi irin na masoya, suna zuwa ne sukayi ido biyu da mahaifiyarta sai yaga ashe wadda sukayi makaranta tare ce har ya ya zaneta da bulala kuma itama mahaifiyar taganeshi.
Kadauka kaine saurayin ya zakaji agurin?.
Kekuma kidauka kece mahaifiya mezaki ce masa?