Taimakon Farko Ga Wanda Maciji Ya SaraWane taimakon farko ake ba wanda

Taimakon Farko Ga Wanda Maciji Ya Sara

Wane taimakon farko ake ba wanda maciji ya sara kafin a kai shi asibiti?

To da yake an fi samun wannan matsala ne a daji ko a gona yana da wuya a ba wanda maciji ya sara taimakon farko ko taimakon gaggawa nan take, sai dai idan akwai mutane a tare da shi a lokacin.

Bugu da kari, kamata ya yi a ce akwai layukan kar-ta-kwana na ma’aikatan agaji na hukumomi da masu zaman kansu wadanda mutum ko shi kadai ne zai buga ya yi bayani a kai masa agaji nan take.

A ’yan kwanakin nan a makarantu da gidajenmu a yanzu akan ji wannan hadari na sarar macizai yana faruwa.

Da an ga wanda maciji ya sara sai a kwantar da shi a sa ya natsu, a kuma tabbatar yana cikin hankalinsa yana magana, don kada ya tsorata ya rikice ya shide.

Wannan yana da muhimmanci don kada rikicewar ta sa guba saurin bin jini.

Daga nan sai a daure wurin da dafin ya shiga (ba saman ba) da tsumma mai tsabta ko yankin tufafin marar lafiyar, don rage zubar jini da kiyaye hawansa zuwa zuciya.

Wadansu sukan ce a kafa kai a tsotse wurin, amma a likitance babu wannan. Sannan sai a garzaya da shi babban asibiti.

An ce babban asibiti saboda can ne ake tunanin za a samu allurar karya dafi, ba a kananan asibitoci ba.

Dokta Auwal Bala

Daga Jaridar Aminiya ta 19 ga Satumba, 2021.

Post a Comment

Previous Post Next Post