* *GYARAN JIKI 1* ****☏+2348037538596*sirrin rike miji*

***** *GYARAN JIKI 1* ****

☏+2348037538596
*sirrin rike miji*

(Fata tayi laushi da sheki)
○ MAN ZAITUN
○ LALLE
○ KURKUR
○ MADARAR RUWA

Zaki hade wannan kayan guri daya sai ki kwaba ki shafe jikinki da fuskarki, idan ya bushe sai ki murje sannan kiyi wanka.

2.
Wannan hadin shi ake cewa kafi delgyeza.

※ KURKUR
※ DILKA
※ ZUMA
※ KWAI
※ LEMON TSAMI

Ki hada su waje daya ki kwaba kamar kwabin lalle amma yafi shi dan ruwa sai ki shafe fuskarki da jikin idan kina so.

Bayn awa 1 sai ki shiga wanka, zaki ga yanda jikinki zai goge.

3.
LALLE
KWANDUWAR KWAI GUDA 3
MANJA COKALI 3
KUR KUR

Sai ki kwaba su guri guda ki shafe jikinki awa

1, sai kiyi wanka da ruwa zalla
Sai ki jika kurku da ruwan dumi ki shafe jikinki, idan ta bushe sai ki sake yin wanka.

**** *KYAN FUSKA* *****

DETTOL
SABULUN GHANA
GARIN ZOGALE
FARAR ALBASA

Sai ki hade su guri guda ki kirba a turmi, ki mulmula ki dinga wanke fuska. 

Zaki ga yanda fuskaki zatayi kyau.

**** *GYARAN FUSKA* *****

Wannan wani hadi ne da kesa fuska tayi haske da annuri ta km kore kurajen fuska.

Ki samu bawon kankana sai ki dinga goge fuskar dashi.

***** *HADIN GYARAN JIKI* ******
AYABA
LEMON TSAMI
TATACCIYAR MADARA
KWAI 1

Ki samu ayaba mai kyau ki bare ko ki matse da hannunki ko ki markada yayi laushi, sai ki zuba madarar ki fasa kwai amma farin zaki zuba sai ki matsa lemon tsami, ki gauraya
sosai sai ki shafa a jikinki yayi awa daya sai kiyi wanka da ruwan zafi.

Idan kika lazumci yin hk kamar kwana 3 zaki sha mamaki.

2.
LEMON TSAMI
BAWON KWAI
KURKUR

Zaki hade su guri guda ki daka sai ki dinga wanka dashi, fatarki zata goge tai kyau.

3.
SABULUN SALO
MAN AUDUGA
DUDU OSUN
DETTOL
LEMON TSAMI

Zaki hadesu waje 1 ki dinga wanka dashi, fatarki zata yi laushi da santsi.

4.
GANYEN MAGARYA
SABULUN SALO

Zaki daka ganyen magarya da sabulun salo ki dinga wanka dashi, yana gyara jiki sosai.

5.
GANYEN MAGARYA
MAN ZAITUN
MAN HABBAT

Ki daka ganyen magarya ki zuba cikin man zaitun ki hada da man habbat sai ki dinda
shafawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post