👉191.Mutane biyu ne suka ci moriyar duniya: Wanda ya rubuta abin da ya kamata a karanta, da wanda ya aikata abin da ya kamata a rubuta.
👉192.Kada ka ɗauka cewa, duk wanda ya yi shiru kurma ne. Wani ya yi shiru ne yana jiran lokaci. Wani ya yi shiru ne don yana nazari. Wani kuma kawaicinsa shi ne maganarsa.
👉193.Abu uku sanin su zai amfane ka:
- Duniya ba a tabbata a cikin ta.
- Kuma babu hutu a cikin ta.
- Sannan ba a tsere ma zargin mutane.
👉194.Idan za ka yi bacci kada ka manta abu uku: Alwala, da karanta Ayatul Kursiyyu, da kwantawa a hannun dama.
👉195.Mai hankali ba ya neman hutu a duniya. Yana tanadin ruhinsa wanda zai je sama bayan mutuwarsa, fiye da yadda yake tanadin gangar jikinsa wadda idan ya mutu za a rufe ta a cikin ƙasa.