URIC ACID. DA MAGANINSAMINENE URIC ACID?

URIC ACID. DA MAGANINSA

MINENE URIC ACID?

Uric acid wani sinadari ne da ake samunsa a cikin jini ta hanyar cin wasu nau'ika abinci masu dauke da sinadarin "purine" mai yawa. Hakka kan janyo hauhawar uric acid din wadda ke bi ta cikin koda kuma hakan yana da nasaba da yanayin aikin Koda. Idan ya kasance kodar bata iya sarrafa wannann sinadarin ta hanyar fitar da shi a fitsari, to mutum zai gamu da jinyar hauhawar uric acid.

Idan sinadarin uric acid ya yi yawa a jikin mutum, ya kan taruwa a gabobi, gwiwowi da duga-dugan mutum ya haifar da ciwon rikewar gabobin ko gwiwowi wato "Gout" a turance. Sannan ya Kan haifar da ciwon Koda samfurin "Kidney stones" idan ba a dauki mataki ba. Sannan zai haifar da dawwamammen ciwon gabobi da gwiwowi da Kuma lalata tsokar da ke kewaye da gabobin.
ALAMOMIN WANNAN CIWO:
1. Ciwon Gwiwowi 
2. Zafin kafafu 
3. Ciwon Duga-Dugai 
4. Ciwon Ga6o6i

ABUBUWAN DA KE JANYO HAUHAWAR SINADARIN
1. Yawan Amfani da "sea foods" kamar su sardines
2. Yawan cin jan nama (Red meat)
3. Yawan cin "organs meat" Kamar su hanta, koda da sauransu
4. Yawan shan barasa ko lemuka masu dauke da sinadarin "alcohol" da shan taba sigari
5. Rashin motsa jiki da tarun kiba (teba)
6. Yawan cin tumatiri (tomato)
7. Yawan cin dankalin turawa (Potatoes)
8. Yawan cin kabeji (cabbage) da sauransu

MAGANI (ULORICIDIC):

Wannan ingantaccen magani an Samar da shi ne domin masu fama da wannan matsala ta hauhawar sinadarin uric acid, wadda ta zama ruwan dare ga mafi yawan tsofaffi, mata, matasa da sauransu.

     1    GANYEN AYABA GUDA 1.
     2.    GANYEN MANGWARO 12.
     3.     TAFARNUWA  dunkule 3

sai a dafa shi sosai Ana shan ruwan maganin safe da yamma.

Kofi daya kafin cin abinci.

ALLAH YA KARA MANA LAFIYA

Post a Comment

Previous Post Next Post