MENENE FIBROID ( curin nama a mahaifa )
Fibroid wata matsalace a
mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama ko ince qululu yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace.
•
Haka zalika Mafi yawan nau'in fibroid da ake samu bayada
alaka da ciwon-daji / kansa (benign/non-cancerous) .
•
Baya ga haka wasu matan sukan samu wannan matsala ta fibroid tun daga loqacin shekarunsu na samun haihuwa wato daga shekara 16 zuwa 45 .
•
♦ ALAMOMIN FIBROID
Wasu daga cikin alamomin sun haÉ—a da:
1. Zubar jinin al'adah na tsawon
lokaci
.
2. Zubar jini baqi a lokutta ko tsakanin lokuttan haila
.
3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki a cikin mahaifa
.
.
5. Ciwon baya daga ƙasan baya
.
6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i
.
7. Rashin jini saboda yawan zubar jini
.
8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki
.
9. Basur maisa tsuguno a bayi saboda rashin fitar bahaya
.
10. Ciwon ƙafa
.
11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyun bane, musamman idan
fibroid din ya girma
1- Matsala lokacin naƙuda
°
2- Matsala yayin fama da juna biyu
°
3- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin
ɗaukar ciki ga mace saboda ƙululun ya toshe/danne wani bangaren mahaif
°
4- Yawan bari/zubewar ciki .
.
N:B:- Iyayena mata , yayyena mata da kuma qannena Yana da matuƙar muhimmanci ga duk mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin dana fada da taimaza taje
asibiti domin a bincika ko kina da matsalar
faibirod . Idan kuma kin riga
kin sani to sai ki nemi magani.
Akwai magungunan da ake warkewa da yardar Allah
.
Allah yabamu lafiya .da zaman lafiya