KAFIN KAYI BACCI.-MAFITAR MATA 01°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

KAFIN KAYI BACCI.
-MAFITAR MATA 01
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

          MAFI YAWAN 'ƳAN WUTA MATA NE
          °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
"Kowane dare ka kasance kana mai yawan roƙon Allah ta'ala ya yafe maka zunubanka kafin kayi bacci, domin haƙiƙa idan kayi bacci ruhinka yana barin gangar jikinka ne, kuma dawowar rayuwarka ba ta da tabbas"
-
"Kada ka zamanto irin mutanen nan waɗanda da zarar sunzo wajen kwanciyar su sai dai kawai su faɗi sharaf kan katifa ko tabarma, babu addu'ar kwanciya bacci sannan kuma babu neman yafiyar Allah abisa zunuban da ka aikata a wannan ranar"
-
"Duk wani mai hankali da tunani yakan yi ƙoƙarin yaga ya nemi yafiyar Allah kafin ya kwanta bacci abisa laifukan da yaaikatawa Allah a cikin ranarsa, waɗand yasan ya aikata da waɗanda ma bai sani ba, domin haƙiƙa ya san cewa idan ya kwanta bacci, to tabbas bai zama lallai a wayi gari dashi ba, to dalilin hakan sai yasa kullum idan yaje gurin kwanciyarsa kafin yayi bacci sai ya nemi afuwar Allah abisa dukkanin ilahirin zunubansa"
-
Telegram channelshttps://t.me/+lNDKpD3Ymv00MDk0 my Telegram group please share me Gloden blogger Facebook page https://www.facebook.com/100090999633409/posts/129445826765405/?substory_index=1593115874530263&app

Post a Comment

Previous Post Next Post