UWAR MIJI!Ayi Sharing Saboda Allah 🔔🔔🔔

UWAR MIJI!

Ayi Sharing Saboda Allah 🔔🔔🔔

Yana dawowa daga aiki Matarshi tayi mai sannu da zuwa ya amsa. Sai yace mata: "Mama bata da lafiya yanzu aka kira aka gayamun, ki shirya yanzu muje mu gaisheta kuma kiyi tunanin me zamu siya mata tsaraba".
Bayan sun shirya sun kama hanya sai ya tambayeta: "Kin yanke shawarar me zamu siya tsaraba? Sai tace: "eh akwai biredi (Bread) da take yawan son taci ko shi aka siya yayi". Sai yace: "ta yaya za'a kaiwa mara lafiya bredi?" "Sai tace to meye basu dashi a gidan ai ba abunda suka rasa". Sai yace: "ai shi kenan". Suka saya suka kama hanya. Toh dama garinsu daya banbancin unguwa ne kawai a tsakanin gidajensu. Suna shiga garin se taga ya kama hanyar gidansu (Matar) gadan gadan basu tsayaba se a kofar gida. Ta tambaye shi: "me yasa muka fara zuwa nan?" se yace: "kamar ya ba duba mara lafiya mukazo ba?" se tace: "Wai wace mama ce bata da lafiya?" ya tambayeta: "mama nawa kika sani?" ta bashi amsa: "maman ka da mama ta". yace: "toh mamar kice bata da lafiya". Toh nan fa zance ya canza, ta zauna a cikin mota tayi zugum. yace: "sauko mu shiga mana". Ai nan ta fara surutai: "wai ze bata kunya, ya za'ayi mahaifiyarta bata da lafiya amma ta kawo mata bredi ai tonan asiri ne". "Na dauka maman kace bata da lafiya ai!"

DARASIN DAKE CIKI
1. Uwa uwa ce koda ta yar tsanace, ki sani da taki uwar da tashi duk d'aya ne tunda dukkan su ya'ya suka Haifa ba dutse ba.

2. In zaki yi magana ki kyautata harshen ki kuma ki daraja furfura.

3. Ki aje duk wani bambanci a gefe, sai ki zauna lafiya in ba haka ba kina tare da wahala da dana sani.

4. Ki zama mai adalci agun Mijin ki ko dan daga Darajar ki da kimar ki da mutuncin ki.

5. Harshe na da illa sosai dan haka Mata a kiyaye dan Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post