Abubuwa Biyar Da Ke Iya Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Gadon Baya.
Da farko, ya kamata a fahimci mene ne faifan ƙashin gadon baya, sannan kuma mene ne aikinsa. Ƙashin gadon baya jigida ce da ta ƙunshi jerin ƙasusuwa har guda 33, tun daga ƙasan ƙoƙon kai har zuwa jelar jigidar inda ta ƙare a cikin ƙugu. A tsakanin kowane ƙashi da ƙashi akwai wannan faifai. Waɗanan fayafayai suna da ɗabi'ar roba ko ɗanko ne, wato suna iya lotsewa idan suka ji nauyi sannan su miƙe idan nauyin ya gushe. Saboda haka ne ƙasusuwan gadon baya ke lanƙwashewa sannan su miƙe ba tare da wata tirjiya ba.
A duk lokacin da wani faifai ya fashe ko kuma ya yi bulli, zai danne laka ko kuma jijiyoyin laka. Hakan yana iya faruwa a wuya ko kuma a baya. A yanzu, za mu mai da hankali kan fashewa ko bullin faifai a ƙasan gadon baya. Saboda a nan ne matsalar ta fi faruwa.
Alamomin fashewa / bullin faifai sun haɗa da:
1. Ciwon ƙafafu: Idan faifai ya samu matsala a baya, bayan ciwon baya sannan kuma ciwon zai riƙa sauka zuwa tsokokin ɗuwawu, cinya, sangalali har zuwa tafin sawu.
2. Idan bullin faifai ya danne laka ko jijiyar laka za a ɗinga jin zogi, raɗaɗi, zafi, dindiris, kamar shokin ɗin lantarki, kamar tafiyar kiyashi ko kuma kamar ana tsitstsira allura a ƙafar.
3. Rauni ko rashin ƙwari: Zuwa wani lokaci, ƙafafu za su fara samun rauni sannan kuma tafiya da sauran ayyukan yau da kullum su fara yin wahala.
Duk da cewa ingancin fayafayan yana raguwa da miƙawar shekaru. Akwai abubuwa biyar da ke ƙara haɗarin fashewa ko bullin fayafayan kamar haka:
1. Ƙiba / teɓa: Ƙarin nauyin jiki na ƙara wa faifai nauyi da wahala.
2. Aiki / sana'a: Ayyukan sana'o'i da ke buƙatar aikin gangan jiki tuƙuru na iya janyo matsalar faifai. Maimaituwar ɗaga kayan nauyi, turawa ko janyo kayan nauyi duka na ƙara haɗarin samun matsalar faifai. Idan kana sha'awar motsa jiki ko atisaye domin gina ƙwanji, kasance ƙarƙashin kulawar likitan fisiyo domin kauce wa samun ciwon baya.
3. Shan taba sigari: Shan taba sigari na rage ingancin aikin faifan.
4. Tuƙi akai-akai: Tuƙi akai-akai tare jijjiga daga abin-hawan na iya yin lahani ga faifai.
5. Rashin motsa jiki: Rashin motsa jiki na iya rage ingancin aikin faifai.
Likitan fisiyo na amfani da ƙwarewa domin rage ciwon da kuma shawo kan matsalar daga tushe. Ci gaba da shan ƙwayoyin rage ciwo ba tare tuntubar likitan fisiyo ba na iya ta'azzara matsalar wanda hakan kuma na iya tilasta yin tiyatar baya daga ƙarshe.
©Physiotherapy Hausa