YAWANCIN MAZA KE JAGORANTAR MAYAR DA MATANSU TSOFAFFI DAGA HAIHUWA ƊAYA.

YAWANCIN MAZA KE JAGORANTAR MAYAR DA MATANSU TSOFAFFI DAGA HAIHUWA ƊAYA.

Mafi yawan maza da zarar sun sauko hakkoki biyu da suka rataya a wuyansu, CIYARWA,  MU'AMALAR AURE.

Da zarar biyun nan sun samu to sauran abubuwan da mata kan buƙata da zai cigaba da alkinta darajarsu da kuma martabasu sai su kauce musu.

Hakika 'yan magana sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka.
Ba ta yadda za a yi kafin ka auro yarinya ta saba da abubuwa daban-daban kamar kayan kwalliya, sutura mai kyau ta ko wanne fanni da suka hada da nau'in daban-daban.
Sai kuma bayan aure ya zamo ba ka mata dinkin sai sallah shi ma kala ɗaya wasu lokutan da zarar ka yi wa yaranka ma da kai kan ka ita sai ta bi rububi.

Kayan-kyale kyale na mata, kayan gyaran jiki da suka hada da turare masu kamshi.
Saya mata pantis masu yawa domin kula da tsafta da kuma Brazeeya wadda ita ma za ta ishe ta, har ma da sauran kayan da za ka so gani.

Amma sai ka bijire ka bar ta koyaushe tana fama da yara, girka abincin da za a ci shara da wanke wanke da dare ka kira ta makwanci.
Ka manta da duk sauran abubuwa ka yi zaton koyaushe za ka rinƙa ganinta yadda kake so.
Shi ya sanya da zarar an yi aure da maza masu irin halayyar nan ko dabi'ar da an haihu sau ɗaya sai ka ga mace ta rakwakwaɓe ta lalace ta zamo tamkar tsohuwa duk ababen da kake gani a baya suna burge ka sai su zamo sun kau.

A nan kuma sai ka fara masifar cewa ta tsufa kai kam yanzu ba ta ishe ka kallo ba, idan ma aka samu wasu sai ka ji sun fara zancen karo kishiya, wasu kuma sai kawai su bayar da takardar saki, wasu su kauracewa matansu a shimfida su daina yi musu magana mai daɗi sai hantara bayan an bar jaki ne kawai ana bugun taiki.

Ya kamata maza su ji tsoron Allah su sani cewa ba zai yiwu ba ka kawo ka bayar ba ka ce kana so ka ga daidai, akwai wanda ma suna gefe da wasu matan suna kashe musu kuɗaɗe masu yawa suna amfani da su wajen su ƙayata jikinsu, sun bar matayensu na sunna a mummunan yanayi da kama.

LIKITAR MA'AURATA..✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post