YI WA MAI GIDA WANKIYI WA MAI GIDA WANKI

YI WA MAI GIDA WANKI
YI WA MAI GIDA WANKI

Kwanakin nan 'yan mata a facebook sun ta da tarzoma akan yi su fa ba dole bane su yi ma miji wanki. Abu kamar wasa maganan ya bi ko ina. Marubuta suka yi ta sharhi da ta'aliƙi. Zuwa yanzu rubutu na ilimi da hankali da aka yi a kan wannan mas'alar sun fito ne daga AbdulHadee Isah Ibrahim da kuma Malama Juwairiyya.

Bari nima in tsoma bakina kaɗan...

1. Wannan debate ɗin akan wanke kayan miji ya taso ne daga cikin mu raw materials wato talakawa. Ba na tunanin wannan matsalar masu kuɗi ko masu mulki ne. Na tabbata A'isha Buhari ba ta yi ma shugaba (Oh! Tsohon shugaba) Muhammadu Buhari wanki. Ban san wani multi millionaire da za a ce matarsa tana wanke kayayyakin ta ba, balle ma na mijinta. Kenan dai ana magana ne akan matan talaka ko karamin ma'aikaci, wadanda ake lallaɓa rayuwa tare. Yau akwai, yau babu.

2. A rayuwar aure, akwai hakkoki na wajibi, akwai na kyautatawa, wadanda ba wajibi ba. Mu ƙaddara cewa yi wa miji wanki kyautatawa ne, kuma kin ce ba za ki yi ba. Ki sani kema akwai hakkoki na kyautatawa da miji yake yi miki su, wadanda ba wajibi ba. Misali; Kuɗin lalle, man shafawa mai kyau, barin ki ki je unguwa, kuɗin biyan napep, amincewa kawayenki ko kannenki su ziyarce ki da dai sauransu. Wadannan ma suna babin kyautatawa ne, ba wajibi ba. Ya za ki ji idan namiji ya janye su saboda kin ki yi masa wanki?

3. Duk malaman soyayya na turawa ko na musulmai sun tabbatar cewa daga cikin alamun soyayya akwai hidima ga masoyi. Daga cikin alamar cewa mace tana son ka akwai yi maka hidima. Daga cikin alamun miji na son ki akwai yi miki hidima. 

4. Wassu matan sun ruɗu da da'awar turawa na "kwato hakkin mace". Amma fa sun manta cewa su ma turawan larura ce ta sa su wannan shiriritar (bayan yakin duniya na farko daga shekarar 1914 zuwa 1918, an kashe miliyoyin mazaje a Turai, sai adadin mata ya fi maza, kuma maza da za su yi aikin sake gina kasashe suka yi ƙaranci, sai aka kirkiro maganan 'yancin mata, domin su fito su yi aiki, kafin wancan lokacin su suke aikin gida, maza kuma su suke fitowa neman abinci). Idan kin ce za ki biye musu, to ki dauki full package ɗin: Haɗa kuɗi za ki yi da mijinki wajen cefane, biyan kuɗin haya, biyan kuɗin makarantar yara da duk sauran ɗawainiyar rayuwa. Kasancewar suna yin haka ne yasa idan auren ya mutu suke da hakkin alimony (a raba dukiyan a tsakaninta da mijin, saboda da gudunmuwar ta aka tara dukiyar).

5. 'Yar uwa, namiji ne ya ke ciyar da ke, ya shayar da ke, ya saya miki sutura, ya biya kuɗin dinki, ya saya miki sabulun wanka. Mai wannan ɗawainiyar shine za ki ji kyashin wanke masa suturarsa, ko da a ce a babin kyautatawa ne? Kina ganin kin yi adalci? Mata masu wannan surutun kawai dama ne suka samu. In da ace za su ji matar ɗan uwansu tana faɗin haka, da su za su tsaya su yi kaca-kaca da ita, har ma su ce ya rabu da ita, ita ɗin 'yar gwal ce? Double standards...

Mata a bi a hankali.

Ba wai ina cewa mace a gidan mijinta baiwa ce ba, a'a, amma dai kowa ya san abinda ya dace...

Post a Comment

Previous Post Next Post