ANFANIN TAFIYA GA JIKIN ƊAN ADAM
---------------------------------------
Yin tafiya a matsayin wata hanyar motsa jiki ya na da faidodi dayawa musamman a wannan lokacin da litan man fetur ke kokarin gagaran talaka Najeriya.
A zamanin da idan kakannin mu suka cika ciki da abinci suna noma domin koma wannan abincin ko kuma su yi tafiya mai nisa zuwa gina ko gida ko sada zumunta. Wannan shi yasa suka samu lafiya sosai kuma basu da hawan jini ko ciwon suga.
Mu a wannan zamanin akwai karancin yin tafiya daga nan zuwa can sannan Bama noma kuma bama motsa jiki. Wannan yasa muke fama da rashin lafiyoyi kala-kala.
Yin tafiya a ƙalla minti talatin a kullum yanada amfani sosai.
Ga wasu daga cikin amfanin tafiya ga lafiyar dan adam:
1. Rage ƙiba.
Ƙiba na kawo kwana jini da ciwon suga da matsalolin zuciya.
2. Kara garkuwa jiki.
Bincike na kimiyya ya nuna cewa garguwar jikin mutum na ƙara ƙarfi idan yana exercise musamman tafiya.
3. Kaifin ƙwaƙwalwa
Yin tafiya yana ƙara karfin ƙwaƙwalwa da kuma tunani da hangen nesa.
4. Lafiyar gaɓoɓi
Yin tafiya yana ƙara lafiyar gaɓoɓi da guiwa.
5. Kwarin ƙashi
Yin tafiya yana ƙara kwari da lafiyar ƙashi. Sai ka ga mutum ya tsufa amma ƙashin sa nada kwari sosai.
6. Hana kamuwa da ciwon suga.
Yin tafiya ya na hana kamuwa da ciwon suga domin tafiya na kona suga kuma ya hana suga taruwa a cikin jini.
7. Hana kamuwa da hawan jini da bugun zuciya.
Tafiya na hana kamuwa da hawan jini. Hakazalika ya na hana samun heart attack ma'ana bugun zuciya saboda tafiya na kona mai da sinadaran da ke iya kawo bugun zuciya.
Allah Ya sa mu dace.