GYARAN GASHI KASHI NA 1

GYARAN GASHI KASHI NA 1

Yadda Za Ki Kula Da Gashinki

Kowane Irin gashi ke gareki yana bukatar wankewa akai-akai da sabulun wankin gashi wanda ya dace da irin gashin da kike dashi (za a ga bayanin haka a rubuce a jikin sabulun) Duk da cewa mata ba su fiye son wanke gashinsu ba saboda gudun kada ya kankance, amma akwai bukatar akalla a wanke shi sau daya a cikin makonni biyu. Tun kafin a wanke gashin, idan akwai amosani, ya kamata a kankare shi, don kada sai an wanke ya rika tasowa yana bata gashin. Sannan akwai bukatar a nemi maganin amosani na musamman.

Bayan wanke gashi sai a bar shi ya bushe, ba a son taje jikakken gashi, sannan sai a shafa masa mai wanda ya yi dai dai da gashin. Idan kitso kika fi so, bayan kin wanke kin shafa masa mai sai ki rangada wanda kike so. Sai dai kuma kada ki bar kitson ya wuce makonni biyu ba tare da kin kwance ba. Idan kuwa baki son kitso, a kullum dole ne ki zauna ki taje gashin tare da shafa masa mai, sannan sai ki daure shi da madaurin gashi (Ribbon) dai dai yadda kike so.

Idan da hali, Zai yi kyau duk bayan wata daya kije salun ki yi masa abin da ake kira steaming, wannan ne zai hana shi karkadewa. Idan kuma ke mai sha’awar yi wa gashi shamfo ce (retourching) shi ma akwai bukatar ki rika maimaitawa a duk bayan watanni biyu. Idan kuma gashinki mai karfi ne za ki rika yi kamar sau daya a wata.Yawan yin shamfo a cikin kwanakin da suka gaza wata guda, masana sun ce akwai yiwuwar zubewar gashi saboda yawan kone shi da ake yi.

Bayan duk kin gama wadannan akwai turaren gashi da za ki rika feshe gashin ki da shi, don ya rika sa shi kamshi na musamman kuma ya kamata ki sani cewa mayukan da ya yi wa wata aiki ba lalle ya yi miki ba, don haka ki kula sosai wajen zabar wanda zai dace da naki gashin.

Post a Comment

Previous Post Next Post