SHIN KUNSAN MENEAMFANIN RUWAN NONON UWA GA JARIRI?

SHIN KUNSAN MENE
AMFANIN RUWAN NONON UWA 
GA JARIRI?

Yayin Da Mace ta haihu takan samu ruwa yana fito wa a nononta wanda ALLAH yayi hakan ne domin jariri ya samu abunci

Ruwan Nono yana da matukar amfani ga uwa da danta kadan daga cikin amfanin Shayarwa da ruwan nono shi ne:

- [ ] RUWAN NONO yana kara wa yaro niima da sinadaran sanya girma fiyeda kowane abuncin da yaro zai sha

- [ ] RUWAN NONO yana bawa yaro kariya daga cutuka manya da kanana: Yaran da suka samu Shayarwa da ruwan Nono sukan samu kariya daga cutuka irinsu Asthma, ciwon sugar da sauransu

- [ ] RUWAN NONO yana inganta garkuwar jikin yaro, da sanya kaifin kwakwalwa

- [ ] RUWAN NONO yana nan ko da yaushe kuma ba sai an siya ba don haka mata masu 
Shayarwa basu da matsalar siyan abuncin Yara 

- [ ] Matan da ke shayarda yayansu da ruwan nono sukan samu kariya daga cutuka irin su cutar daji na nono, ciwon sugar, da kuma hawan jini

Ina fatan matan da basu shayarwa da Ruwan nono zasu gane cewa shayarwa sauki ne kuma rahama ce ga yaro da kuma su baki daya 

Domin Karin bayani a tuntube mu 

Ranakun Awo a asibitin best choice Hospital suna 

Wednesday-Laraba 
Friday- Jummat
Sunday-Lahadi

#bestchoicehospital #breastfeeding #breastmilk #newbornbaby #motherlove #motherslove

Post a Comment

Previous Post Next Post