SHIN KANA FAMA DA CIWON GABOBI (Joint pain) TSAYA KA JI ABUN DA KAN JAWO CIWON GABOBI

SHIN KANA FAMA DA CIWON GABOBI (Joint pain) TSAYA KA JI ABUN DA KAN JAWO CIWON GABOBI

Gaba (joint) wata mahadace da kashi ke haduwa
CUTUTTUKAN DA KAN JAWO CIWON GABOBI

Cutuka irin su Lupus, Arthritis, osteoarthritis, gout, septic arthritis suna kan gaba wajen jawo ciwon gaba. 

LUPUS: Yanda wannan cuta ke jawo ciwon gaba shine.
A jikin dan Adam akwai halittun da ke bawa jiki kariya (immune system) in aka sa mu aka si wanann halittun da suke bawa jiki kariya suna suke yakar cells  dake gabobin mu wanda hakan yakan jawo ciwon gabobi

OSTEOARTHRITIS: wanan lalura ta ciwon gabobi yafi yawa  a mutane masu Shekaru. Domin kuwa wanan cutar osteoarthritis takan cinye wannan farar fatar dake lullube da kashin guiwa. Wannan fatar ce ka sanya guiwa ta samu kariya. Hakan yakan sanya ciwon guiwa.

RHEUMATOID ARTHRITIS : shima lalura ce dake ke sanya halittun dake bawa jiki kariya su cinye fatar dake bawa gabobin mu kariya 
 Wanda hakan kan sanya ciwon gabobi 

GOUT: cutace dake sanya Uric Acid ya daskare a cikin gabobin mu. Shi uric Acid abune dake ya kamata a ce ya fita daga  jikin mu ta fitsari. Amma yayin da cutar gout ta kama mutum to zai kasance Uric Acid ya daskare a cikin jikin wanda hakan kan jawo ciwon gabobi 

IDAN HAR KANA FAMA DA CIWON GABOBI TO BA KAI KADAI BANE KUMA CUTACE DA KE DA MAGANI

DON HAKA YANA DA KYAU A GA LIKITA DOMIN TABBATAR DA ME KE JAWO CIWON GABOBIN 

ALLAH YA TSARE

#bestchoicehospital #healthylifestyle #jointpain #gout #lupus #arthritis #healthiswealth #jointhealth

Post a Comment

Previous Post Next Post