WASU DAGA CIKIN AMFANIN MAN RIDI A JIKIN DAN ADAM

WASU DAGA CIKIN AMFANIN MAN RIDI A JIKIN DAN ADAM 



1. Gyara fata da inganta lafiyar ta.

2. Kara girman gashi da launin bakin sa.

3. Kariya daga ciwon-daji (Cancer).

4. Gyara fatar jarirai da sanya su natsuwa da bacci.

5. Hana rubewar hakori, kogon hakori da sauransu.

6. Kariya daga ciwon asma da cututtukan numfashi.

7. Rage hawan-jini.

8. Rage yawan sinadarin "Cholesterol".

9. Kariya daga ciwon-suga.

10. Inganta lafiyar kwalkwalwa da sauransu.

DOMIN SAMUN LAFIYAYYAR FATA;

Ana hada Man Zaitun da Man Ridi a mayar da shi abin shafawa a wata daya fatar jikin Mutum zatayi kyau kuma ta samu kariya daga Fungal Infection.

CIWON MARA;

Ana shan cokali 2 safe da rana da dare dan maganin ciwon mara.

CIWON CIKIN DA BAYAJIN MAGANI; 

DA KURAJE MUSAMMAN NA KAZWA;

A samu sabulun Zaitun a riqa wanka da ita idan aka bushe sai a shafa Man ridi a kalla ayi haka sau 2 a Rana tsawon sati daya.

CIWON SIKILA;

Ana hada man Ridi da Zuma a riqa bawa mai matsalar yana shan cokali biyu safe da rana da dare har tsawon wata 2.

BASIR MAI TSIRO;

A samu Sassaken Bagaruwa da 'ya'yan ta a tafasa da ruwa idan suka tafasa idan sun rage zafi sai a zauna cikin ruwan tsawon minti 15 idan aka fita a shafa Man ridi ayi haka sau 2 kowacce rana
tsawon kwana 10.

ASHMA;
A rika shan cokali 2 safe da rana tsawon sati 3.

ULCER;
A samu Man Ridi a hada da Madara a riqa sha da safe kafin aci komai haka da dare bayan anci komai sai asha awa daya kafin a kwanta.

KUMBURIN JIkI;
Ana shafa man ridi duk bayan anyi wanka da kuma in za'a kwanta bacci.

SOSHE SOSHE SABODA YAWAITAR MAJINA KO MATACCEN JIN:

Sai a saka cokali 2 duk lokacin da za'aci abinci sannan kuma a shafe jiki da shi amma wajen shafewa dole sai an hada da Man Zaitu.

CIWON MARA LOKACIN FARA AL'ADA:

Ana hada cokali daya na garin Ridi da cokali daya na man Ridi da madarar gari a sha sau 3 kullum In shaa Allahu za'a samu sauqi. Insha allahu

A tura wannan sako zuwa ga yan uwa domin su amfana

Post a Comment

Previous Post Next Post