ALLAH BAYA TAUSAWA WANDA BAI TAUSAYAWA MUTANE.

.ALLAH BAYA TAUSAWA WANDA BAI TAUSAYAWA MUTANE.

Yau duk magidancin dake samon kasa da dubu shittin awata (60,000) to yana acikin masifar rayuwa.

Da Wannan muke kira ga shuwagabanni da hukumumi kan suji Tsoron Allah akan rayuwar wadanda suke mulka.

Sbd da kasancewar wannn kididdigangan lisafin rayuwar Talakan Kasar.

Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa 250 Maggi ɗaya Naira 10 Biredi Wanda Mutum biyu zasu iya Ci Naira 250 Taliya 450 ..

Sabulun Wanka 200 Na Wanki 200 Kuɗin Ruwa Jarka ɗaya naira 50 a ƙalla ka sayi jarka biyu kullum naira ɗari..

Sai Ka Buga lissafi a sati ɗaya ,Kai da amarya da ƴa"yan" 3, ƙannin ka 1,kwa lashe Kwano Huɗu na shinkafa Kuɗinta Zai Kama naira 1850 ×4 Zai kama Naira 7400..

Biredi 250 a ƙalla ku siya sau biyar a sati Kuɗinka Zai Kama 1250..

Taliya a ƙalla ka sayi Guda Uku a satinnan kuɗinka zai kama 1350..

Kuɗin Ruwan sha na wanki dana wanka a ƙalla jarka biyu a rana naira ɗari sau 7 ya kama ɗari bakwai a sati..

Sabulun wanka da na wanki ,Maggi , Kayan Miya, Gas ko gawayi , Man girki Kuɗinsu zai Kama Naira 6000 A sati..

Shinkafar Sati Ɗaya - 7400
Biredi na Sati Ɗaya- 1250
Taliyar Sati Ɗaya-1350
Kuɗin Ruwa-700
Su kayan miya da sabulun wanka da wanki, gawayi ko Gas , Man girki -6000

Total ɗin Sati ɗaya duka- 16,700
Total ɗin wata ɗaya-66,800

Wannan lissafi kada ka manta ba'a saka wasu abubuwa ba da yawa kamar kuɗin NEPA, magani na rashin lafiya, kuɗin kayan kwalliya, auduga ta mata yayin Al'ada, Kuɗin taransifot  na zuwa wajen aiki ko kasuwa na maigida, Ƴar madara ta watsawa a shayi, ɗan naman miya, sugar, Lipton,kudin karan waya ,gasu nan dai birjik..

Shi yasa Muke gayawa Gwamnati da babbar murya ,
Da tashiga cikin ganin jamaa suna samun rayuwa ta ci da Koshi  kamar yadda suke da iyalansu. kaga dai lissafin dubu sittin ma tayi kaɗan, wannan kuma shine ƙarshen lissafi wanda ba kowacce Iyali nema zata iya yadda ta zauna a haka ba😭😭😭😭😭🤲

Copy

Post a Comment

Previous Post Next Post