Matuqar kana son iyalin ka, kana jin dadin zama da ita.....................................
Tabbas ba zai rageka da komai ba dan ka kira ko ka kallenta ka furta mata :-
💝Kana sonta
❣️Kayi kewarta
💝Ka ji dadin ganinta
❣️Tayi kyau
💝Ka gode
❣️Tana ƙoƙari
💝Kana jin dadin zama da ita
❣️Kana jin daɗin ka za da take ma
💝Ilimi, tunani, hankali, sadaukarwanta suna burge ka
❣️Iya girkinta
💝Yadda take mu'amalantar 'yan uwanka
❣️Yadda take lura da gida da yaran ku.
💝Yadda kake jin daɗin mu'amalan aure da ita
❣️Yadda zaka bada lokaci wajen wasanni dan ganin ta samu gamsuwa a shimfiɗa
💝Bata lokacin ka dan hira da tattauna abunda ke damunta ko ya shafe rayuwar ku.
Tabbas, Furta irin wadannan kalamai ga mace na sa zuciyanta taushi a gare ka, yana sa taji daɗi, yana rage mata damuwa, yana sata nitsuwa akan ka, ya kuma ƙara mata kuzari wajen ƙara kyautata mu'amala gare da wadda suka shafe ka.
Karki manta ba mace kaɗai ke da buƙatar yawan jin haka ba, tabbas yadda kike son ji ire iren wadannan abubuwa dan samun kwarin guiwa haka maza ma na son ana faɗa musu irin wadannan kalaman, dan gwargwadon abunda zaki ji in a ranki in an faɗa miki gwargwadon abunda zai jin a zuciyar sa shima in aka fada masa haka.
Tabba wadannan kalamai ne da ma'aurata da dama ke da ƙishin jin su daga abokan zaman su, kar ku hana kunnuwan ku da zukata ji da ɗanɗanon garɗin wadannan kalaman dan girman kai da kauyan ci.
In baku faɗa musu ba wa zaku faɗa ma ?
In baku faɗa musu yanzu ba sai yaushe zaku faɗa ?