MAGUNGUNA NA MUSAMMANAmfanin Tafarnuwa Ga Jikin Dan’adam

MAGUNGUNA NA MUSAMMAN

Amfanin Tafarnuwa Ga Jikin Dan’adam
1.Ciwon Mara Lokacin Al’ada Idan mace tana ciwon mara ko ciwon ciki a lokacin al’ada ko jinin yarika yi mata wasa, ta samu zuma ludayi biyu

(2) ta hada da man tafarnuwa ludayi daya
(1) in an hada sai ta rika sha cokali biyu
    (2) da safe biyu (2) da yamma. In Allah ya yadda zai bari.

2. Matar Da Jini Ya Ki Dauke Mata Ta rika shan man tafarnuwa babban cokali sau hudu (4) a rana. In sha’Allahu zai dauke.

3. Riga-Kafin Ciwon Nono Ga Wadda Tahaihu Ana cin dabino guda bakwi (7) a sha man tafarnuwa babban cokali sau uku (3) a rana zuwa kwana uku (3). Ana dacewa da izinin Allah in an gwada.

4. Daurewar Ciki Ko Mara Bayan Haihuwa A samu ruwa mai zafi kofi daya (1) a zuba man tafarnuwa babban cokaki daya (1) a sha so uku (3) a rana har kwana uku (3).

5. Yawan Lalacewar Ciki Ko Yawan Bari A samu kwan agwagwa a soya da man tafarnuwa a bai wa matar ta ci sau biyu (2) A rana har kwana (7).

6. Tsawon Gashi Da Hana Shi Karyewa A samu man kwakwa a hada da man zaitun da man tafarnuwa a rinka shafawa A kai, amma man tafarnuwa ya fi yawa ana shafawa.

7. Tari Ko Wanne Iri A samu man tafarnuwa da man zaitun da Zuma mai kyau a hada su a waje guda, zumar ta dan fi yawa. Ana jijjigawa a sha cokali biyu (2) da safe da rana dayamma. In sha Allahu za a samu sauki.

9. Hawan jini Ko Rashin Yin Barci Mai Kyau A samu garine Tafarnuwa rabin ludayi sai a samu zuma mai kyau a hada su waje daya ana gaurayawa ana shan cokali babba daya so uku (3) a rana. Sannan kuma a samu man tafarnuwa ana shafawa a jikinka. Alla zai ba ka lafiya.

10. Sihiri Ko Maita Ko Sammu Ko Aljani Ko Mutum Mai Yawan Mafarkin Tsoro A samu man tafarnuwa da man zaitun da habbatussauda da zuma a hada su waje daya a jijjigawa sai a sha cokali biyu (2) sau uku (3) a rana ana kuma shafa man tafarnuwa sau uku (3) shi ma a rana. Kar a gaji don Allah kuma kar a raina.

Post a Comment

Previous Post Next Post