Ko Kun San? Amfanin Kanwa A Jikin Dan’adam ?:

Ko Kun San? Amfanin Kanwa A Jikin Dan’adam ?:

 

Kanwa na daga cikin ma’adinai da aka samu kuma ake yin amfani da ita cikin abincin da muke ci.

 Haka kuma kanwa a jikin mutum ko kuma dabba na taimakawa gaya da kara wa jikinsu lafiya. Kamar yadda kwararren likitan nan George Krucik ya bayyana da cewa “tun da ba jiki ne yake samar da kanwa ba, don haka ne ake bukata a yi amfani da ita da yadda ta dace a cikin abinci. 

Rashin amfani da kanwa kan iya haifar da barazana ga lafiyar jiki. Haka kuma in aka yi amfani da ita da ya wuce kima zai iya haifar da matsala ga jiki”. 

Ga jerin wasu daga cikin amfanin kanwa a jikin dan’adam:

● Kanwa tana dai-daita ruwan jikin dan’adam.

● Tana kara wa jijiyar jiki kwari da warware shi.

● Kanwa tana kara wa zuciya lafiya da kuma kuzari.

● Tana rage kasala jiki.

● Tana rage kamuwa da cutar hawan jini.

● Kanwa tana taimakawa wajen narkar da abinci nan take.

● Tana taimakawa wajen rage bugun jini.

● Kanwa tana taimakawa wajen sarrafa abinci masu gina jiki a jikin dan’adam har da wasu dabbobi.

● Tana taimaka wa masu fama da mura.

● Kanwa tana cire tsamin abinci idan miya ta yi tsami sai asamu a jika kanwa a zuba a ciki ‘yar kadan.

● Tana kuma kwantar da kwarnafi. Da wannan ne ma Hausawa ke amfani da wani karin magana wajen nuna amfanin kanwa inda suke cewa “kanwa ta kar tsami, kwarnafi ya kwanta.

 ━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Amfanin Karas A Jikin Dan’adam 🌱

Amfanin karas dangane da lafiyar dan’Adam da kuma samun kariya, daga cututtuka musamman irin cutar daji, inda take shiga cikin jikin mutum tana lalata mahiifa, dalilin sanadiyyar lalacewar mahaifa kuma yana sabbaba kamu da ciwon daji.

Karas yana dauke da wasu sinadarai masu yawan gaske, kamar Mangenes, Aion, Calsiom, Phosphorus, Better Carotene, Alpha carotene, yana kuma dauke da cikakken Sinadarin Bitamin A, da Bitamin C, da Kuma Maadinin Anti-odidants, wanda yake bama jikin dan’Adam kariya da Kuma garkuwar.

Karas yana kara lafiya idanu sosai ta fuskar kara gani da kuma hasken idanu.

Karas yana magance tare da bada kariya ga kamuwa da cutan daji.

Kamar yadda Likitoci masana suka bayyana cewa, a duk lokacin da aka kunna kukan gas a cikin gida ko aka kunna wutar icce ko aka kunna fitila ko kuma taba to dole sai an samu cuta ta kewaya wannan gurin, kuma ita ce take shiga cikin jiki tana lalata mahaifar dake cikin jikin mutum, wannan dalili yana daya daga cikin abin da yake haddasa wa asami cutar daji. Don haka masu gida ku rika saya wa iyalanku karas suna ci, ko kuma a yi garin sa ana sha da zuma ko ruwan shayi. Ko a rika sakawa a cikin abinci ko a rika nikata ana shan ruwanta ko a dafa.

Garin Karas idan mai cutar daji yana shan to yana kone cutar na daji in sha Allah.

karas yana dauke da cikakken sinadarin Bitamin A, dukkan 100 gram na karas ya tattaro 8.285 micro gram na better carotene. Kuma yana dauke da pulapuniad cikakke wanda yake aiki wajen kare fatar jiki, da kuma matsalar hunhu da kare su daga cututtutka wadanda ake shakar su ta hanyar odygen zuwa cikin jiki.

Karas yana yakar ciwon zuciya, sa’annan yana da asiri ga masu fama da ciwon zuciya da kuma ciwon hawan jini.

Karas yana dauke da sinadarin mai saka wajiki karfi sosai.

Karas yana baiwa hanta kariya daga cututtutka wadanda suke kewaye da ita.

Yana kara lafiyar hakora da kuma dasashi. Yana hana Tsutsar hakori. Yana taimakawa wajen magance warin baki.

Yana gyara fatar jiki. Yana hana fitowar kuraje.

Post a Comment

Previous Post Next Post