Domin mata 05Malaria in pregnancy..

Domin mata 05

Malaria in pregnancy..

Malaria: rashin lafiya ce da ake samunta sanadiyyar cizon macen sauro, wadda take sakawa mutum kwayoyin cutar malaria a cikin jini.

A na samun cutar ne a sanadiyar kwayoyin cutar da macen sauro ke zubawa mutum acikin jini.

Kwayar cutar da take kawo malaria a Najeriya ana kiran ta da Plasmodium Falciparum.

Mata masu juna biyu suna daga cikin mutanen da idan malaria ta kama su rayuwar su yana cikin hatsari.

Malaria tana kawo waÉ—annan matsaloli ga mata masu juna biyu:
1- IUFD (Mutuwar yaro kafin a haife shi
2- Abortion (Brin ciki)
4- Preterm Delivery (Haihuwan Bakwaini)
4- A karshe uwar da yaron dukka za su iya rasa rayuwar su.

Kuma malaria tana iya kawo:
1- Rashin jini a jiki 
2- Matsalar kwakwalwa
3- matsalar Ciwon zuciya
4- Matsalar huhu da oda
5- Kumburi ko fashewar spleen .
6- Yana saukan da suga ( Hypoglycemia

Alamomin malaria sun hada da:
1- Zazzabi
2- Ciwon kai
3- Tashin Zuciya
4- Amai
5- Gudawa
6- Ciwon jiki
7- Atini
8- Dachin Baki
9- Rashin Cin Abinci
10- Rashin Karfin jiki.
11- Kasala
12- mutun yaji ya rasa abinda yake masa dadi.

Kariya daga kamuwa da cutar malaria:

1- Mace juna biyu ya kamata tafara zuwa awun juna biyu (ANC) akan lokoci.

Lokocin awu ana bada maganin kariya daga kamuwa da cutar malaria ga mata masu juna biyu. Ana bada:

A- Fansider (sulfadoxine-pyrimethamine) wani magani ne wanda ake bawa mata masu juna domin kariya daga cutar Malaria.

Ana bada maganin ne da zarar mace cikin ta yakai watanni hudu ( 16weeks), sannan abada 2nd dose a 20 - 22 weeks sannan a bada 3rd dose a 26 weeks ( akalla ana so a samu tazarar sati 4 sakanin ko wacce dose). Kuma anaso mace tasha wannan maganin a kalla so takwas (8) kafin tahaihu.

B- Sannan ana bada gidan sauro, da wassu shawarwari da mace za tabi ta kare kanta daga kamuwa da cutar malaria.

Idan nafara jin alamomin malaria zan iya shan maganin Malaria?

A'a, a matsayin na mace mai juna ba ko wacce magani ya kamata kisha ba ko da ace kin tabbatar kina da malaria. Domin mafi yawan magungunan malaria mata masu juna biyu bai kamata suyi amfani da ita ba.

Haka kuma shan magani barkatai ba bisa ka'ida ba yana kawo resistance ( ma'ana kwayoyin cuta su Dinga jure maganin, baya kashe su.)

Abinda ya kamata kiyi shine kiyi kokorin zuwa asibity a miki abinda ya dace.

Sai mun hadu a rubutu na gaba...

Post a Comment

Previous Post Next Post