game da abinda ke kawo maikon fuska

GAME DA ABINDA KE KAWO MAIKON FUSKA(OILY SKIN A TURANCE).
Rukky BashirMarch 07, 2023
 
GAME DA ABINDA KE KAWO MAIKON FUSKA(OILY SKIN A TURANCE).

Daya daga cikin hikimar halittar fata a jikin dan Adam dama sauran halittu shine don su baiwa jikin kariya. Ita fatar dan adam(human skin) kamar yadda muka sani, Itace take rufe da tsokar jiki, jijiyoyi, ligaments(bansan yadda Zan kira shi da Hausa ba) da sauran muhimman sassan jiki.



Kasantuwar chudanyar ta da muhalli, sai ta kasance tana dauke da wani irin kakkarfan garkuwa(immunity) Wanda yake kare jiki daga hadarin raguwar ruwa a jiki(water loss) da Kuma shigar wasu kwayoyin cutar. 



Game da dalilan da yasa fatar dan Adam take yin maiko(oily) kuwa, ga kadan daga cikinsu; 



1- Gado(Heredity): Idan ya kasance mutum yana dauke da genes a jikin sa wanda ya samo asali daga daya daga cikin iyayen sa, wanda shi wannan gene din yake da alaka da Wannan matsalar, to akwai possibility na shima fatar sa ta rika fitar da maiko fiyeda kima!



2- Chanjin yanayi(Change in weather condition); Kamar yadda muka sani, yanayin zafi yafi yanayin sanyi sanya fatar jikinmu Tayi maiko fiyeda kima. Wannan ajiye take! 



3- Shan wasu magungunan (Medication); Yawancin mata masu amfani da magungunan kayyade iyali(family planning) sunada possibility na suga fuskar su tana yawan yin maski koda basu shafa mai ba. 



4- Chanjawar sinadaran jiki(Hormonal changes); Akwai sindarai da yawa a jikin dan Adam, Chanjawar wasu daga cikinsu zai iya kawo wannan matsalar. Misali, idan karamin yaro ya Fara balaga, zamu ga fuskarsa tana yin maski fiyeda kima. Wanda hakan yana nuna cewa sinadaran jikin sa suna kokarin adopting chanjin da jikin sa yake samu.



5- Stress; Watau lokacin da jiki ya jigata da yawa, ta hanyar zurfafa tunani dake wahalar da kwakwalwa ko Kuma wani strenuous aiki, fuska ko nace fatar jiki takan rika tatso Mai dake cikinta fiyeda lokacinda babu stress din. Zamu fahimci haka idan muka tuna yadda wasu suke fitar da zufa(sweat) cikin hanzari duk lokacin suka shiga wani tashin hankali wanda ya kai su ga tsakanin tunani.



Wadannan sune kadan daga cikin dalilan dake sanya fatar jiki ta rika yin maski more than normal. Akwai wasu tarin dalilan, wadanda ilimi da nazari na basu Kai na sansu ba. 



In sha Allahu Kuma a rubuta na gaba, zanyi magana akan yadda za a iya magance Wannan matsalar cikin sauki.



Allah Yasa mu dace.

Allah Ya bamu lafiya, da zaman lafiya da abinda lafiya zata ci.

Post a Comment

Previous Post Next Post